Mutum huɗu sun rasu yayin da ƙasar wajen haƙo ma’adinai ta rufta a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masu aikin haƙar ma’adinai guda huɗu sun gamu da ajalinsu a lokacin da ƙasar wani wurin haƙar ma’adinai ta rufta akansu a yankin Baban Rafi da ke Ƙaramar Hukumar Ɓokkos a Jihar Filato. Al’amarin ya auku ne a ranar Talata yayin da mutanen suke tsaka da aiki a wajen.

Shugaban Matasan Ɓokkos, Daniel Tula ne ya ya tabbatar da wannan labari ga gidan Talabijin na Channels a wata hirar tarho, inda ya ce mamatan sun haɗa da maza da mata biyu-biyu.

A cewarsa, mutanen sun rasu ne sakamakon ruftawar wani sashe na ƙasar ramin da suke gudanar da aikin nasu, sannan kuma daga bisani ‘yan uwansu sun yi musu jana’iza. Ya bayyana al’amarin a matsayin irinsa na farko da suka taɓa gani a yankin, lamarin da ya haifar da fargaba kan amincin masu aikin haƙo ma’adinai a yankin.

Shugaban matasan ya kuma ce har yanzu ana ƙoƙarin gano ainihin dalilan da suka sabbaba faruwar al’amarin, amma ya tabbatar da cewa mamatan suna aikin neman ƙarfe ne a lokacin da iftila’in ya rutsa da su.

Saidai, Rundunar ‘Yan sandan Filato ta ce ba ta samu wani rahoto ba a hukumance kan al’amarin, kamar yadda kakakinta, SP Alfred Alabo ya shaida wa Channels. Ya ƙara da cewa, a mafi yawancin lokaci masu aikin haƙar ma’adinai ba sa kai wa ‘yan sanda rahoton faruwar irin waɗannan al’amura, wanda ke sa hukumar take gagara gano ainihin abin da ya faru cikin sauƙi, yana mai cewa za su fitar da rahoto na musamman da zarar sun samu cikakken bayani a kai.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da fargaba kan halin aminci da ƙalubalen da ke tattare da ayyukan haƙar ma’adinai a ƙauyukan sassan jihar Filato.

By Babaji

Leave a Reply