Gwamnatin Kebbi ta nemi Malami ya janye kalaman sa kan rusa wani gini a Birnin Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana cewa ba ta da hannu a rushe wani gini da ke kan titin Sani Abacha da ke garin Birnin Kebbi da jagoran jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Abubakar Malami ke yayatawa.

Jaridar News Point ta bayyana cewa
Kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Yakubu Ahmed ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar da ke garin Birnin Kebbi. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi ta nisanta kanta daga rushe wannan ginin da ke kan titin Sani Abacha da ke cikin garin Birnin Kebbi wanda hasali ma a ke danganta shi da mallakar wani makusancin Malami kamar yadda waɗansu ke bayyanawa.

Yakubu ya ƙara da cewa gwamnatin Kebbi ba ita ce ke da mallakar wannan wajen ba kuma ba ta da wata alaƙa da wannan wajen kuma ba ta da hannu wajen rusa wajen. Alhaji Ummaru Gulumbe ne ya mallaki wajen kuma ya fito a kafafen yaɗa labarai ya bayyana cewa shi ne ya sa aka rushe ginin.

Kwamishinan ya nuna rashin jin daɗin sa bisa ga yadda ɗan takarar na jam’iyyar ADC ya saka gwamnatin Kebbi a cikin wannan lamarin.

Ya kuma nemi Malami da mutanen sa musamman Wamban Koko da su janye kalaman su kan gwamnatin jihar Kebbi.

By ukarofi

Leave a Reply