An kama masu yin rajistar NIN ta jabu a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Rajistar Shaidar ɗan ƙasa (NIMC) ta ce ta kama wasu mutane tare da ƙwace kayayyakin aikin rajista ba bisa ƙa’ida ba, yayin wani samame da ta kai cibiyoyin da ke gudanar da rajistar Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) da sauya bayanan jama’a ba tare da izini ba, a Gwagwalada da wasu sassan Babban Birnin Tarayya Abuja.

Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Hukumar, Kayode Adegoke, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Ya ce sashen sa ido kan bin ƙa’idoji da aiwatar da dokoki na hukumar (ICEU) ne ya jagoranci samamen.

Adegoke ya bayyana cewa wannan samame na daga cikin ƙoƙarin da hukumar ke yi na dakile rajistar NIN ba bisa ƙa’ida ba, sauya bayanan mutane ba tare da izini ba da kuma karɓar kuɗaɗe ta hanyar tilas. Sanarwar ta ce, “Hukumar NIMC ta lura cewa yawancin matsalolin da mutane ke fuskanta dangane da Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) na faruwa ne sakamakon kauce wa ƙa’idojin rajista da aka tanada a hukumance.”

Hukumar ta ƙara jaddada cewa ba a yarda a gudanar da rajistar NIN a ko’ina ba, illa a cibiyoyin da ta amince da su. Haka kuma, dole ne a yi duk wani gyara ko sauya bayanan mutum ta shafin intanet ɗin hukumar da aka tanada domin gudanar da wannan aiki. Sanarwar ta ce, “Ana iya yin rajistar NIN ne kawai a cibiyoyin da hukumar ta amince da su, yayin da za a iya sauya bayanai ta shafin nan: self-serɓice modification.nimc.goɓ.ng.”

Hukumar ta kuma shawarci masu NIN da su sauke manhajar NINAuth daga shagon manhajojin iOS ko Android domin kare lambobinsu, buga takardar shaidar NIN da kuma amfana da sauran matakan tsaro da manhajar ke samarwa.

Adegoke ya kuma rawaito Babbar Daraktar Hukumar NIMC, Abisoye Coker-Odusote, tana sake jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci karɓar kuɗaɗe ta hanyar tilas ko duk wani hali na rashin ɗa’a daga ma’aikatanta ba. Ta ce, “Domin samun sahihan bayanai, ku ziyarci shafin www.nimc.goɓ.ng ko ku bi sahihan shafukan hukumar na kafafen sada zumunta. Haka kuma, ana iya kiran layin kyauta na hukumar ta lamba 0800 0616 462.”

By ukarofi

Leave a Reply