Majalisar Dokokin Nijeriya na nazarin ƙarin kujeru mata zuwa 74

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa Majalisar Dokoki ta ƙasa na nazarin wani ƙudiri da ke neman samar da ƙarin kujeru 74 na musamman ga mata a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, a wani ɓangare na bitar Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 da ake gudanarwa.

Bamidele ya kuma bayyana cewa Kwamitin Bitar Kundin Tsarin Mulkin ya gabatar da shawarar samar da ƙarin kujeru uku na musamman ga mata a kowace Majalisar Dokokin Jiha. Ya ce za a ware waɗannan kujeru ne ga mata zalla, ba tare da rage ko ƙwace ko ɗaya daga cikin kujerun da ake da su a yanzu ba.

Shugaban masu rinjayen ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin makon shari’a na shekarar 2026 da ƙungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya reshen Jihar Ekiti (FIDA) ta shirya.

Taron, wanda Ayobami Olowoyo-Richards ta jagoranta, an gudanar da shi ne ƙarƙashin taken: “Adalci a duniya mai sauyawa: Tunkarar sababbin ƙalubalen da ke shafar mata da yara.”

Bamidele, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Bitar Kundin Tsarin Mulkin 1999, ya ce an tsara ƙudirin ne domin faɗaɗa damar mata na shiga harkokin siyasa da gudanar da mulki. Ya ce, “A halin yanzu, Majalisar Dokoki ta ƙasa na duba wani ƙudirin doka da ke neman yin gyare-gyare ga wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999, domin samar da kujeru na musamman ga mata a Majalisun Dokoki na ƙasa da na Jihohi, da kuma sauran abubuwan da suka shafi hakan.

“An tsara wannan shawara cikin tsari mai zurfi da kulawa. Tana neman ƙara kujeru 37 a Majalisar Dattawa da kuma wasu 37 a Majalisar Wakilai. Idan aka amince da ita a ƙarshe, kowace jiha a tarayyar Nijeriya, har da Babban Birnin Tarayya, za ta samu ƙarin kujera guda ɗaya a kowace Majalisa daga cikin Majalisun Dokoki na ƙasa. An kuma tsara tsarin ya ɗauki tsawon shekaru 16, wato zagayen zaɓe huɗu, kafin a sake gudanar da cikakken nazari a kansa. Wannan tanadi na sanya wa dokar wa’adin ƙarewa ne, domin tabbatar da ɗorewar shirin tare da ba da damar bunƙasa al’adar siyasa mai bai wa kowa dama a hankali.”

Bamidele ya ce Majalisar Dokoki ta ƙasa na tattaunawa da Majalisun Dokokin Jihohi domin samun amincewarsu, kasancewar hakan na daga cikin sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya tanada kafin gyaran ya fara aiki.

Ya bayyana kudirin a matsayin wani gagarumin sauyi da ya shafi ƙasa baki ɗaya, ba wani shiri na wata jam’iyya ko ɓangaren siyasa ba. Ya ce ware mata daga wuraren yanke shawara na raunana tsarin dimokuraɗiyya da ya kamata ya wakilci kowa. Ya ce, “Dimokuraɗiyyar da ke ware fiye da rabin al’ummarta daga teburin yanke shawarar da za ta tsara makomarsu, a mafi ƙarancin hali, dimokuraɗiyya ce mai nakasu; a mafi muni kuma, tana kama da mulkin wasu tsirarun mutane a ɓoye.”

Shugaban masu rinjayen ya ce ƙudurin Majalisa ta 10 na ganin an samar da ƙarin damar shiga harkokin siyasa ga mata ya samu ƙarfafa ne sakamakon fafutukar da manyan jami’an gwamnati suka dade suna yi, ciki har da uwargidan Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu. Ya ƙara da cewa, Majalisar Dokoki ta ƙasa na kuma nazarin wasu matakai da za su tallafa wa mata, yara da kuma mutanen da ke da buƙatu na musamman, ta fuskar ayyukan kiwon lafiya, samun damar ilimi da shirye-shiryen kare jin daɗin al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply