Daga USMAN KAROFI
Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar da sabon shawarwarin lafiya dangane da annobar cutar Ebola da ke ci gaba da yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC). Hukumar ta ce Najeriya na ƙara matakan shiri domin kare ƙasar daga duk wata barazanar da ka iya tasowa daga annobar.
NCDC ta shawarci matafiya da ke shigowa Najeriya daga ƙasashen da ake samun yaɗuwar Ebola da su cike takardar bayanan lafiya (Health Declaration Form), a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa sa ido da gano masu yiwuwar kamuwa da cutar. Sai dai hukumar ta ce a halin yanzu matafiya daga sauran ƙasashe ba sa buƙatar cike wannan takarda. Haka kuma, ta buƙaci jama’a su kasance cikin taka-tsantsan tare da neman kulawar likita cikin gaggawa idan sun fara nuna alamomin da suka yi daidai da na Ebola.
A cewar bayanan da aka fitar, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta samu jimillar mutane 7,672 da aka tabbatar sun kamu da cutar zuwa ranar 20 ga Satumba 2026, yayin da mutane 3,699 suka mutu. An kuma ce akwai marasa lafiya 886 da ke kwance a wuraren killacewa, yayin da sabbin mutane 58 suka kamu da cutar, sannan aka samu ƙarin mace-mace 23 tun bayan rahoton da ya gabata.
Sabbin masu kamuwa da cutar 58 sun fito ne daga larduna huɗu, inda Ituri ke da 38, North Kivu 14, Haut-Uélé biyar, sannan Tshopo mutum ɗaya. NCDC ta ce za ta ci gaba da sa ido kan yadda cutar ke yaɗuwa tare da duba da sabunta matakan shiri da mayar da martani bisa sauyin yanayin annobar. Hukumar ta kuma jaddada cewa tana amfani da sa ido, shiri da matakan kariya bisa hujjojin kimiyya wajen kare lafiyar al’ummar Najeriya.
