
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniyar Nijeriya, Festus Keyamo ya bayar da kariya ga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke jagorancin su David Mark a Jam’iyyar ADC da soke takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 na tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar.
A wani rubutu ta sahihin shafinsa na X a ranar Juma’a, Keyamo ya bayyana cewa akwai buƙatar a riƙa mu’amalantar hukunce-hukuncen shari’o’i da dalilan gaskiya da hujjoji a madadin amfani da fahimtar al’umma, matsin siyasa ko cece-kuce.
Ministan ya caccaki masu sukar hukuncin tare da yin gargaɗin cewa farmakar alƙalai ko yunƙurin wulaƙanta shari’a don hukunci bai dace da abin da suke so ba ba daidai ba ne. “Bai dace ku riƙa zagin alƙalai ko yi musu sharri ba don ba su yi abin da kuke so ba. Sammai ba za su rikito ba idan aka ce wani Atiku Abubakar bai shiga sahun ‘yan takara ba a zaɓen 2027,” inji shi.
Keyamo ya kuma ce, ADC jam’iyya ce da ke wanzuwa a Nijeriya da ainihin jagorori da mambobinta waɗanda su ma ‘yan Nijeriya ne kamar ‘yan tsarin jagorancin da kotu ta rushe suke.
Ministan ya yi wannan tsokaci ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan karɓar hukunce-hukuncen shari’o’in kotu, musamman waɗanda suka shafi rikice-rikicen siyasa da halin da jam’iyyu suke amsa musu. Matsayar ministan ta tunatar da hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli na zaɓen gwamnonin Bayelsa na 2020 da na Zamfara na 2019, wanda jam’iyya mai mulki APC ta sha kaye a dukkaninsu.
Rikicin jam’iyyar ADC ya ɗauki wani salo ne a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026 a lokacin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta soke jagorancin na su David Mark da takarar Atiku yayin da zaɓukan 2027 ke cigaba da ƙaratowa.
