
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An garzaya da wata ‘yar shekara 14 mai suna Amina Ya’u zuwa asibiti sakamakon raunukan harbin bindiga da ta samu bayan wani farmaki da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka ƙaddamar a wasu gonaki da ke ƙauyen Majelisa a iyakar jihohin Nasarawa da Filato.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa masanin harkar tsaro, Zagazola Makama cewa al’amarin ya auku ne a ranar 5 ga Nuwamba da misalin ƙarfe 6:30 bayan samun rahoton harbe-harben bindiga a yankin.
A cewar rahoton, sojojin Sashe na 9 na Atisayen Operation Enduring Peace (OPEP) da aka jibge a Jenta, sun yi hoɓɓasa wajen zuwa ƙauyen yayin da suka samu kiran gaggawa kan al’amarin. A yayin haka ne suka samu yarinyar cikin jini sakamakon raunukan da ta samu, saidai maharan sun arce a lokacin da dakarun suka isa wajen.
Sakamakon bincike ya nuna cewa wasu da ake zargin mayaƙan makiyaya ne suka buɗe wuta ga manoma biyo bayan rashin cimma yarjejeniya akan gudanar da harkokin kiwo a yankin.
A cewar Makama, jami’an tsaro suna aiki tare da jagororin Fulani domin taimakawa wajen zaƙulo waɗanda suke da hannu a laifin tare da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka. Sannan dakarun tsaro sun faɗaɗa ayyukan sintiri a yankin domin daƙile yiwuwar sake aukuwar irin harin ko faɗaɗa rikicin.
