Tinubu zai samar da mashigar tolget masu amfani da fasahar zamani a manyan titinan Nijeriya – Ministan Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar sake gabatar da mashigar tolget masu amfani da fasahar zamani domin kakkaɓe ayyukan garkuwa da mutane da wasu miyagun laifuka a manyan titinan Nijeriya, kamar yadda Ministan Tsaro, Christopher Musa ya bayyana.

Ministan ya faɗi haka ne a wani taron da jam’iyya mai mulki APC ta shirya a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Shirin Shugaban Ƙasa akan Motoci Masu Mafani da Iskar Gas da Lantarki (PiCNG& EV), Ismaeel Ahmad a Abuja.

Christopher Musa ya bayyana cewa, baya ga amfani da mashigar wajen samun kuɗin shiga ga gwamnati, za kuma su riƙa aiki a matsayin shingen binciken tsaro, inda kayayyakin fasaha za su riƙa ganowa da tantance motoci ba tare da neman su tsaya saboda biyan kuɗaɗe ba.

Bayan tambayar sa kan ko hakan zai sa masu zirga-zirga su riƙa bayar da kuɗi yayin amfani da mashigar, ministan ya ce, hakan zai taimaka wajen tara wa gwamnati ƙarin kuɗin shiga don warware matsalolin rashin tsaro ta hanyar amsar kuɗaɗe ƙalilan daga gare su.

A cewarsa, wajibi ne tsarin ya samu goyon bayan fasahar da za ta iya gano motoci, ta lambobin rajistarsu da biyan kuɗaɗe ta na’ura. Kazalika, ministan ya yi kira ga a samar da tsarin gano ababen hawa da fuskar mutane ta hanyar fasaha domin taimaka wa hukumomin tsaro a harkokinsu na yaƙi da aikata miyagun laifuka.

By Babaji

Leave a Reply