Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An kammala shirye-shiryen gudanar da bikin karrama fitattun ’yan jarida a Nijeriya na bana, wanda Sakatariyar ƙasa ta ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta shirya, inda tsofaffin ’yan jarida Alhaji Abdulkadir Ahmed Ibrahim (Kwakwatawa), Azubuike Ishiekwene da wasu fitattun ƙwararrun kafafen yaɗa labarai za su kasance cikin waɗanda za a karrama.
Rahotonni sun ya bayyana cewa bikin zai karrama ƙwararrun ’yan jarida waɗanda gudummawarsu ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin yaɗa labarai a Nijeriya. A cikin wata sanarwa da Sakataren kwamitin shirya bikin, Olayide Awosanya, ya sanya wa hannu ta hanyar lantarki, masu shirya taron sun bayyana cewa Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Francis Oborevwori, wanda zai halarta a matsayin Babban Baƙon Musamman, ana sa ran zai gabatar da jawabin buɗe taron.
Bikin mai taken “ƙarfafa Dimokuraɗiyya Ta Hanyar Aikin Jarida Mai ɗaukar Nauyi da Kyakkyawan Shugabanci” zai gudana ne a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, a otal ɗin Abuja Continental. Shugaban Kwamitin Shirya Bikin na ƙasa, Otunba Gbenga Onayiga, ya ce bikin na bana zai samu halartar fitattun ƙwararrun ’yan jarida da masana harkokin sadarwa.
Ya ce: “A wannan karon, muna son mu yi bikin karrama kanmu. Muna karrama abokan aikinmu waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu ga aikin jarida, tare da amincewa da jarumtaka, sadaukarwa, jajircewa, ƙwarewa da gudummawar da suka bayar ga wannan sana’a mai daraja.”
A cewarsa, “Bikin karrama fitattun ’yan jarida ya bambanta da sauran bukukuwa. Ba ɗaya daga cikin irin bukukuwan bayar da lambobin yabo ba ne. Hanya ce ta musamman da NUJ ke amfani da ita wajen nuna godiya da karrama hidima, juriya, sadaukarwa da amincin waɗanda ake karramawa tsawon shekaru.”
Onayiga ya yaba wa Shugaban NUJ na ƙasa, Comrade Alhassan Yahaya, da tawagarsa bisa ci gaba da gudanar da shirin, wanda aka tsara domin karrama fitattun ’yan jarida tun suna raye, maimakon jira har sai sun rasu. A cewar masu shirya bikin, nau’o’in ayyuka da ƙwarewar waɗanda za a karrama na nuna irin zurfin gogewarsu, ilimin hukumomi da ƙwarewarsu a fannin aikin jarida. Sun bayyana su a matsayin fitattun taurari da suka yi fice a wannan sana’a mai daraja tare da zaburar da matasa masu tasowa.
Daga cikin waɗanda za a karrama akwai Alhaji Abdulkadir Ahmed Ibrahim, FNGE, wanda aka fi sani da Kwakwatawa. Ya taɓa zama Mataimakin Shugaban NUJ na ƙasa daga 1990 zuwa 1997, sannan ya zama Shugaban Majalisar NUJ ta Jihar Kano daga 1981 zuwa 1983. A halin yanzu, shi ne Sakataren kuma mamba a Kwamitin Amintattu na ƙungiyar Tsofaffin ’Yan Jarida ta Kano.
Sauran waɗanda za a karrama sun haɗa da Chief Eric Teniola, tsohon Daraktan Yaɗa Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya; tsohon babban ɗan jarida kuma tsohon Darakta-Janar na Hukumar Gidan Rediyon Tarayya ta Nijeriya (FRCN), Lauya Yusuf Nuhu, FNGE; Olusegun Adeniyi, Shugaban Kwamitin Editoci na THISDAY; Chief Abia Onyike, tsohon Mataimakin Shugaban NUJ na ƙasa; da Ayo Adewuyi, Babban Daraktan Labarai na hedikwatar NTA da ke Abuja. Haka kuma, akwai Mai Martaba Oba Rotimi Obamuwagun, tsohon Mataimakin Shugaban NUJ na ƙasa; Mukhtar Gidado, tsohon Mataimakin Shugaban NUJ na ƙasa kuma Mai Bai wa Gwamnan Jihar Bauchi Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a; Hajiya Tabitha Sani Kangiwa; Ignatius Nwachukwu; Mrs Toro Oladapo, tsohuwar Shugabar ƙungiyar Mata ’Yan Jarida ta Nijeriya (NAWOJ); da Franz Ndulue.
Sauran sun haɗa da Martins Oloja, FNGE, tsohon Manajan Darakta na jaridar The Guardian da ke Legas; Azubuike Ishiekwene, FNGE, Babban Mataimakin Shugaban Kamfanin Leadership Media Group kuma Edita-in-Chief; Kingsley Uranta na Channels Media Group, Legas; Olori Janet Mba Afolabi, Olori na Masarautar Apomu kuma mawallafin mujallar SCROLL; da Bayo Bodunrin, FNGE, na DAAR Communications, Abuja.
Jerin sunayen ya kuma ƙunshi Uzoma Livingstone Isiakpu, tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Jihar Imo; Adeyinka Amosu, tsohon Daraktan Ayyukan Legas na Hukumar Gidan Rediyon Tarayya ta Nijeriya; Jubrin Bello Kwami; Ayinde Soaga, tsohon Babban Manajan NTA Minna; Sumna Sambo, Daraktan Labarai kuma Editan Siyasa na ARISE NEWS TV, Legas; da Hajiya Aisha Abdullahi Jao.
