Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala aikin Umara da samun damar yin addu’a a cikin Ka’aba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Abuja a daren Laraba bayan kammala aikin Umara a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, inda ya yi addu’o’i na musamman domin zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da ci gaban Nijeriya.

Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa jirgin shugaban ƙasar ya sauka a sashen jiragen shugaban ƙasa na filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 8:53 na dare, lamarin da ya kawo ƙarshen ziyararsa ta ibada a ƙasar Saudiyya.

Tinubu ya shafe kwanaki biyar a Saudiyya, bayan ya bar Abuja a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila, ne ya tarbe shi a filin jirgin, tare da gwamnoni biyar, ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.

Gwamnonin da suka tarbe shi sun haɗa da Uba Sani na Jihar Kaduna, Ahmad Aliyu na Jihar Sakkwato, Babagana Zulum na Jihar Borno, Umar Namadi na Jihar Jigawa da Mai Mala Buni na Jihar Yobe.

Sauran jami’an da suka halarta sun haɗa da Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa; ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle; da Daraktan Sashen Protocol na Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Ibrahim Sule Dan Agundi.

Tinubu ya tashi daga filin jirgin sama na King Abdulaziz da ke Jeddah da misalin ƙarfe 5:13 na yamma agogon Saudiyya, bayan kammala aikin Umara.

Kafin barin Saudiyya, shugaban ƙasar ya gana da mataimakin gwamnan yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud, a fadar baƙi ta masarautar.

Jami’in Saudiyyar, tare da jakadan Nijeriya a ƙasar Saudiyya, Yakubu Gambo, da Jakadan-Janar, Ambasada Muazam Ibrahim Nayaya, sun raka shugaban ƙasar zuwa filin jirgin sama.

A lokacin zamansa a Makkah, Tinubu ya gudanar da ibadun Umara, ciki har da yin ɗawafi a ɗakin Ka’aba mai alfarma da ke cikin Masallacin Harami, inda ya yi addu’o’i ga Nijeriya da al’ummarta.

Babban abin da ya ja hankali a ziyarar shi ne damar musamman da aka ba shugaban ƙasar da tawagarsa ta shiga cikin Ka’aba a ranar Lahadi, inda suka gudanar da sallah da addu’o’i na musamman.

A cikin ɗakin mai alfarma, Tinubu ya roƙi Allah da ya ba Nijeriya zaman lafiya mai ɗorewa, tsaro, haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki. Ya kuma roƙi Allah ya ba shi hikima, ƙarfi da juriya wajen sauke nauyin da ke kansa na shugabancin ƙasa.

Da yake tsokaci kan wannan ziyara, Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da aikin gina Nijeriya, samar da ƙasa mai wadata, zuba jari a makomar matasa da kuma ƙoƙarin bunƙasa ƙasa.

Ya kuma yi addu’ar cewa bambancin addini, ƙabila da al’adu na Nijeriya ya zama tushen ƙarfi da wadata ga ƙasa, maimakon ya zama sanadin rarrabuwar kai.

“ƙarfinmu yana cikin bambancinmu, kuma muna ci gaba da gina ƙasa bisa wannan ginshiƙi domin samar da makoma mai kyau da tsaro,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya kuma nuna godiya ga Mai Kula da Masallatai Masu Alfarma Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mai Jiran Gado kuma Firaminista, Mohammed bin Salman, bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa da tawagarsa.

Ya bayyana damar shiga cikin Ka’aba a matsayin wata babbar karramawa da ba kasafai ake samu ba, wadda kuma ke nuna kyakkyawar alaƙar addini da abota tsakanin Nijeriya da Saudiyya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ da aka tantance a ranar Litinin, shugaban ƙasar ya ce ya yi amfani da wannan tafiya ta ibada wajen neman albarkar Allah ga Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply