Ba mu samun isassun jiragen haya don yaƙin neman zaɓe – Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya ce shi da sauran ’yan siyasar da ke shirin tunkarar zaɓukan gama-gari na shekarar 2027 na fuskantar ƙalubalen samun jiragen sama masu zaman kansu na haya domin zirga-zirgar yaƙin neman zaɓensu daga wannan wuri zuwa wancan.

Mista Akpabio ya danganta wannan matsala da rashin ƙarfin kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu a Nijeriya wajen biyan buƙatar zirga-zirgar jiragen sama.

Ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar a ranar Talata, lokacin da sanatoci ke muhawara kan wani ƙuduri da ke neman tabbatar da aiwatar da Yarjejeniyar Sufurin Jiragen Sama Tsakanin ƙasashe Biyu (Bilateral Air Services Agreement – BASA) tsakanin Nijeriya da China.

ƙudurin, wanda Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) ya gabatar, ya buƙaci gwamnatin Bola Tinubu da ta sake tattaunawa kan yarjejeniyar domin bai wa kamfanonin jiragen saman Nijeriya damar gudanar da zirga-zirgar jiragen kai tsaye zuwa China.

Da yake amfani da lokacin bukukuwan ƙarshen shekara, musamman watan Disamba, wajen misalta matsin lambar da ake fuskanta a ɓangaren sufurin jiragen sama na ƙasar, Akpabio ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta magance ƙalubalen da kamfanonin jiragen saman cikin gida ke fuskanta.

“Ku jira watan Disamba ku ga rudanin da zai faru. Hatta kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu ba za su iya biyan buƙatar ba. A irin wannan lokacin yaƙin neman zaɓe, ba ma iya samun jiragen sama masu zaman kansu da za mu yi haya. Ya kamata aƙalla mu iya roƙon gwamnatin tarayya ta duba wannan matsala domin rage wa kamfanonin jiragen sama wahala,” in ji shi.

Akpabio ya kuma tuna lokacin da Nijeriya ke da kamfanin jiragen sama na ƙasa, wato Nigerian Airways, wanda ya ce yana jigilar mahajjata daga Nijeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajji.

Ya ce a wancan lokaci kamfanin yana da jirage tsakanin 32 zuwa 40, waɗanda ke gudanar da zirga-zirga zuwa wurare daban-daban, inda ya tambayi yadda harkar sufurin jiragen sama ta Nijeriya ta lalace har ta kai ga halin da take ciki a yanzu.

“Mun kasance muna da jirgin sama da ke jigilar mutane zuwa Saudiyya da sauran wurare. A wancan lokaci, Nigerian Airways na da jirage kusan 32, har ma da 40, waɗanda ke tashi daga wannan wuri zuwa wancan. To, ta yaya muka kai ga wannan hali?” ya tambaya.

Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa Nijeriya na buƙatar kamfanin jiragen sama na ƙasa da zai riƙa ɗaga tutar ƙasar.

’Yan siyasa da amfani da jiragen haya masu zaman kansu

Amfani da jiragen sama masu zaman kansu da ’yan siyasar Nijeriya da manyan jami’an gwamnati ke yi ya zama ruwan dare, musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe da tafiye-tafiyen aiki, duk da tsadar kuɗin hayar irin waɗannan jirage.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman na shugaban ƙasa, ’yan takara da jam’iyyunsu kan kashe miliyoyin nairori wajen yin hayar jiragen sama domin zirga-zirga tsakanin jihohi, halartar gangami, tarukan yaƙin neman zaɓe da sauran ayyukan siyasa cikin ƙayyadadden lokaci.

’Yan takarar shugaban ƙasa musamman kan dogara da jiragen haya domin isa wurare da dama a faɗin ƙasar, saboda yawan buƙatar tafiye-tafiye da kuma buƙatar tafiya tare da mataimakansu, jami’an tsaro da tawagogin yaƙin neman zaɓensu. Kuɗin hayar jiragen na bambanta ne bisa nau’in jirgin, nisan tafiya, tsawon lokacin haya da sauran yanayin gudanar da aikin.

Rahotannin da aka wallafa a intanet sun yi ƙiyasin cewa kuɗin hayar jiragen sama masu zaman kansu a Nijeriya na tsakanin dala 5,000 zuwa 7,000, kwatankwacin kusan naira miliyan 6.6 zuwa miliyan 9.3 a kowace sa’a ta tashi, gwargwadon nau’in jirgin, yawan fasinjojin da zai ɗauka, hanyar tafiya da yanayin gudanar da aikin.

Wannan na nufin ’yan siyasa za su iya kashe tsakanin dala 30,000 zuwa 42,000, kwatankwacin kusan naira miliyan 38.8 zuwa miliyan 55.7, a tafiyar da za ta ɗauki sa’o’i huɗu zuwa shida.

Wannan al’amari bai taƙaita ga ’yan takarar Shugaban ƙasa ba. Gwamnoni, ’yan majalisun tarayya, ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati ma na amfani da jiragen sama mallakarsu ko waɗanda suka yi haya wajen tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje. Sau da yawa suna danganta hakan da ƙarancin lokaci, buƙatun tsaro da kuma sauƙin tafiya ba tare da dogaro da jadawalin jiragen kasuwanci ba. Wasu manyan jami’an gwamnati kuma na da damar amfani da jiragen sama mallakar gwamnati ko na fadar shugaban ƙasa wajen gudanar da ayyukansu.

Haka kuma, ana amfani da jiragen haya masu zaman kansu wajen tafiye-tafiyen ƙasashen waje. Bayanai da rahotannin da aka wallafa a baya sun nuna yadda manyan jami’an gwamnati suka yi amfani da irin waɗannan jirage a tafiye-tafiyensu zuwa ƙasashen waje.

Misali, tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya shaida wa wata kotu a Birtaniya a shekarar 2026 cewa ya amince da amfani da jiragen sama masu zaman kansu da tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, ta yi a wasu tafiye-tafiyenta na ƙasashen waje.

By ukarofi

Leave a Reply