Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke jagorancin ADC tsagin su David Mark da takarar Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya gudanar da hukuncin da ya soke jagorancin tsagin su Sanata David Mark a Jam’iyyar ADC da rushe dukkan wasu matakai da ya ɗauka a madadin jam’iyyar.

Cikin ababen da kotun ta soke har da matakin tsayar da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Atiku, wanda da fari INEC ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, ya zaɓi tsohon Gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi a matsayin abokin tafiyarsa.

Saidai, a hukuncin da Mai Shari’a Lifu ya yi a yau Alhamis, ya ayyana cewa jagorancin Sanata David Mark ga kwamitin riƙo na ADC haramtacce ne duk da cewa shi ya shirya zaɓen fidda gwanin ɗan takarar da ya bai wa Atiku nasarar zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

An yanke wannan hukunci ne kan ƙarar da fusataccen tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa maso Gabas, Nafi’u Bala ya shigar, inda ya ƙalubalanci hanyoyin da aka bi wajen karɓe iko da jagorancin jam’iyyar da ɓangaren na su Mark ya yi.

Ya bayyana cewa, bayan tsohon Shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu ya yi murabus, shi ne wanda ya cancanci zama jagoran jam’iyyar. Akan haka ya buƙaci kotun da ta soke dukkan wasu matakai da jagorancin nasu ya ɗauka. Waɗanda aka zayyano a matsayin su aka shigar ƙara sune, ADC, INEC, Sanata Mark, Ogbeni Rauf Aregbesola da kuma Cif Ralph Nwosu.

Haka kuma, ya roƙi kotun da ta haramta wa Mark da Aregbesola ayyana kansu a matsayin Shugaba da Sakataren jam’iyyar, yana mai cewa zamansu a muƙaman ya saɓa wa dokokin jam’iyyar da na zaɓe.

Wannan hukunci ya sa ADC ta ƙudiri aniyar ɗaukaka ƙara, kamar yadda Sakataren Walwala na Ƙasa, Nkemakolam Ukandu ya bayyana. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Nijeriya a ranar 16 ga Junairun 2027.

By Babaji

Leave a Reply