2027: INEC za ta goge rajistar masu zaɓe miliyan 1.5 da aka yi ba bisa doka ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta ce ta shirya tsafa domin fara aikin goge rajistar masu zaɓe guda miliyan 1.5 da ta gano cewa an yi su ne ba bisa ƙa’ida ba daga cikin jaddawalin masu rajista na ƙasa gabanin zaɓukan 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana haka yayin karɓar baƙuncin wata tawaga da ta kai wa hukumar ziyarar ban-girma a hedikwatarta da ke Abuja, ranar Laraba. Wakilin Musamman na Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya na Yammacin Afirka da Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya na Yammacin Afirka da Yankin Sahel (UNOWAS), Mista Leonardo Santos ne suka jagoranci tawagar.

Amupitan ya ce, fasahar zamani ce ta taimaka wa jami’an hukumar wajen gano wuraren da aka shigar da ire-iren waɗannan sunaye. Ya bayyana cewa, aikin gogewar wani ɓangare ne na tabbatar da sahihancin jaddawalin rajistar masu zaɓen domin warware matsalolin wuraren da ake da ke inkarin akansu.

Za a wallafa jaddawalin ƙarshe ne a ranar 15 ga Disambar 2026. A cewar farfesan, INEC ta yi wa ‘yan ƙasa miliyan 103 rajistar zaɓe, inda matasa da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 34 suka samu kusan kaso 29 na jimillar adadin masu rajistar.

Kazalika, ya ce hukumar za ta cigaba da amfani da na’urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) don tantance masu zaɓe da shafin INEC Result Viewing Portal (IReV) domin bai wa al’umma damar sanin sakamakon zaɓe a kowace rumfar zaɓe.

By Babaji

Leave a Reply