Tinubu ya dawo Nijeriya bayan kammala Umrah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A daren wayewar Alhamis Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ibadar Umara a Makka, Saudiyya, inda ya yi addu’o’i na musamman ga zaman lafiyar Nijeriya, tsaro, haɗin kai da nasarori ga al’ummar ƙasa, kamar yadda Manhaja ta ruwaito a baya.

Shugaban Nijeriyar ya isa filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe ne da misalin ƙarfe 8:53, lamarin da ya kawo ƙarshen ziyararsa ta Ƙasa Mai Tsarki. Ya dawo Nijeriyar ne bayan shafe kwanaki biyar. A ranar Alhamis, 29 ga Oktoba Shugaban ya bar Abuja ya garzaya Saudiyya.

Yayin dawowar tasa, Tinubu ya samu tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila, tare da wasu gwamnonin jihohi biyar, ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.

Gwamnonin sune Uba Sani na Kaduna, Ahmad Aliyu Sokoto na Sakkwato, Babagana Zulum na Borno, Umar Namadi na Jigawa, da kuma Mai Mala Buni na Yobe.

Sauran sun haɗa da Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa; Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle; da Babban Daraktan Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Ibrahim Sule Ɗan-Agundi.

By Babaji

Leave a Reply