NYSC ta musanta sahihancin shaidar tsohon minista, Nnaji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Harkokin Matasa Masu yi wa Ƙasa Hidima NYSC, ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa takardar shaidar kammala hidimar ƙasa da ake danganta wa tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha Geoffrey Nnaji ba ita ta bayar ba, tana mai bayyana ta a matsayin ta bogi kuma ta zayyano matsaloli huɗu a tare da ita da suka bambance ta da irin waɗanda take bayar wa.

NYSC ta bayyana haka ne ta bakin Mataimakin Daraktanta na Reshen Bada Shaida, Yusuf Abubakar Jumare, wanda ya tsaya a matsayin shaidan masu gabatar da ƙara na biyu (PW2) a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik. Jumare ya bayyana cewa, binciken da reshensa ya gudanar ya nuna cewa takardar shaidar NYSCn da ake taƙaddama akanta ba daga hukumar aka samo ta ba.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta maka Nnaji ƙara ne bisa tuhume-tuhume da suka shafi lamuran bogi a takardun karatunsa da badaƙalar wasu maƙudan kuɗaɗe a wata shari’a mai lamba FHC/ABJ/CR/379/2026. Jumare ya ce sun gudanar da binciken bayan ICPC ta buƙaci a yi haka, ƙarƙashin jagorancin lauyan da ke kare masu ƙara, Jimoh Abdulmumuni.

Ya zayyano ababe huɗu da ke nuna cewa ba NYSC ba ne ta bayar da takardar shaidar. Abu na farko, ya ce lambar shaidar, wadda aka ce an bada ta ne a shekarar 1985, na ɗauke da harafin “A” a farko, wanda ya ce hukumar ba ta fara aiki da shi ba sai a 1990. Na biyu, lambar kira ta Call-up na da lambobi huɗu – 0137 – yayin da salon lambobin da aka bayar a 1985 mai ɗauke da guda biyar ne.

Sannan, takardar ta nuna cewa hidimar watanni 13 aka yi a madadin watanni 12 na shekara da aka saba. Abu na ƙarshe, ya ce Shugaban NYSC na lokacin Nnaji ya ce ya yi hidima, bai sanya hannu akanta ba. Ya bayyana cewa, ana kiran shugaban NYSC da “Director” ne daga lokacin da aka kafa hukumar har zuwa lokacin da Nnaji ya yi iƙirarin yin hidima, inda shaidar da ake ƙalubalantar take ɗauke da “National General”.

A nasu ɓangaren lauyoyin masu kare ƙara sun faɗa wa kotun cewa, za su warware inkarin da suke da su kan hujjojin da aka gabatar a wani lokaci, inda suka bayyana cewa ba a gabatar musu da takardun da ke tabbatar da tuhume-tuhumen ba. Lauyan masu gabatar da ƙara ya ce za su gabatar da su nan gaba duba da cewa bai jima da karɓar ragamar shigar da ƙarar ba.

By Babaji

Leave a Reply