
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Malamin islamiyar nan da aka sace wa ɗalibai daga gonarsa a ƙarshen mako, Malam Aminu Baƙo, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kira jagororin ƙauyen, inda suka nemi a biya sama da Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansarsu. Baƙo ya kuma fitar da sunayen ɗaliban sannan ya yi kira ga sojoji da su gaggauta ɗaukar matakin ceto su.
Saidai ya ce babu wani tallafi da makarantar ko iyalansu suka samu domin ceto yara 15 ɗin tun lokacin da abin ya faru baya ga ƙoƙarin ‘yan bijilante. Baƙo ya shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa Shugaban Ƙaramar Hukumar Rafi na riƙo da DPOn ‘yan sandan yankin ne kaɗai suka kai musu ziyarar jaje tun faruwar al’amarin. A cewarsa, bayan ziyarar mutane biyun, an bar iyalan da dogara da ƙoƙarin ‘yan bijilante na farauto masu garkuwar.
Ya bayyana cewa, sakamakon binciken da aka samu na sirri daga ɓangaren ‘yan bijilanten ya nuna cewa ɗaliban suna nan acikin Jihar Neja, inda aka ajiye su a wani keɓaɓɓen waje da tarin ‘yan bindiga suke, yana mai cewa matakin soji ne kaɗai zai iya ceto su. “Mun ji cewa suna nan acikin Jihar Neja, rufe a wani gida, ƙila ma babu abinci. Mu na cikin damuwa. Mu na buƙatar hukumomi su taimaka mana su ceto su,” inji shi.
Malamin ya ce yana cikin mawuyacin halin matsi daga ɓangaren iyayen yaran tun lokacin da aka sace su musamman kan a wane hali ‘ya’yan nasu suke. Ya ce, ‘yan bindigar sun kira jagororin ƙauyen a yammacin ranar Litinin, inda suka buƙaci a biya sama da Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.
Ya shaida wa LEADERSHIP sunayen ɗaliban da aka sacen daga gonar marasarsa kamar haka: Hassana Isah, Aliya Ahmad, Hajara Musa, Hauwa’u Abubakar, Halima Yahaya, Asma’u Jamilu, Radiya Salisu, Aminatu Salisu, Aisha Bello, Rahinatu Sani, Aminatu Alhassan, Nafisa Ayuba, Bilkisu Adamu, Salaha Abdullahi da kuma Hajara Salisu.
