Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura (OD) ya bayyana cewa nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na Sanatan Zamfara ta Arewa ta gaskiya ce kuma mafi rinjayen mambobin kwamitin zaɓe da uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta turo ne suka gudanar da zaɓen.
Da yake jawabi ga manema labarai a gidansa da ke Kaura Namoda a ranar Talata, Sanata Tijjani ya zargi cewa shugaban kwamitin, Dr. Auwal Abdullahi Aliyu, an sace shi kuma wasu ɓatagari masu ƙin bin tafarkin dimokuraɗiyya sun tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
A cewarsa, Shugaban Kwamitin an yi garkuwa da shi kuma shi kaɗai ya sanar da sakamakon bogi inda ya ayyana Sanata Sahabi Ya’u Kaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen, yayin da mafi yawan mambobin kwamitin suka haɗa kai suka tattara ainihin sakamakon kuma suka ayyana shi (Tijjani Yahaya Kaura) a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Sanata Ƙaura ya bayyana yin garkuwa da Shugaban Kwamitin a matsayin yunƙurin murƙushe dimokuraɗiyya, wanda masu zaɓe ba za su taɓa lamunta ba.
Ya yi watsi da ikirarin abokan hamayyarsa na cewa an ayyana Sanata Sahabi Ya’u a matsayin wanda ya lashe zaɓen, yana mai cewa irin wannan aiki haramun ne, babu inganci kuma ba shi da wani tasiri.
“Sanarwar da mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi aka ware shi ya yi ba za ta tsaya ba. Ainihin sakamakon da mafi yawan mambobin kwamitin suka tattara kuma suka sanar ne suka gudanar da zaɓen bisa ga kundin tsarin mulkin jam’iyya da ƙa’idojin zabe. Wannan shine sakamakon da ke nuna ra’ayin jama’a,” in ji Ƙaura.
Ya ce mambobin jam’iyyar APC a Zamfara ta Arewa sun fito ƙwansu da kwarkwatarsu domin gudanar da haƙƙinsu na ɗan ƙasa ta hanyar zaɓen sa a matsayin ɗan takarar Sanata a babban zaɓen 2027.
Tsohon Sanatan ya nuna matuƙar godiyarsa ga masu zaɓe bisa amincewa da suka nuna masa na wakiltar mazaɓar Sanatan Zamfara ta Arewa a Majalisar Dokoki ta ƙasa.
“Ina matuƙar godiya ga al’ummar Kaura Namoda, Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi bisa goyon baya da suka bani da kuma jajircewarsu wajen kare ƙuri’unsu. Wannan nasara tamu ce baki ɗaya kuma ta dimokuradiyya ce,” in ji shi.
Don haka Sanata Ƙaura ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a kowane mataki da su mutunta ra’ayin masu zaɓe a mazaɓar Sanatan tare da sanarwar da mafi yawan mambobin kwamitin zaɓen fidda gwani suka yi.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da zama masu bin doka da oda da kwanciyar hankali, yana mai tabbatar musu da cewa zai kare muradan su ta dukkan hanyoyin da suka dace.
