Wasiƙa ga masu ganin cewa kashe wanda ya saɓa musu a fahimta shi ne hanyar tabbatar da gaskiya da cimma buri.
Ya ku masu ganin cewa harsashin bindiga zai iya kashe tunani, yaƙi zai iya kashe hujja, zubar da jini kuma zai iya kawo aarshen saɓani!
Ku tsaya ku yi tunani na ɗan lokaci. Ku tambayi kanku: Wane ne ya ba ku tabbacin cewa idan kun kashe mutum, kun kashe abin da yake wakilta? Wane ne ya gaya muku cewa idan kuka rufe bakin wani, kun sa duniya ta daina jin saƙonsa? Kuma wa ya tabbatar muku cewa mutumin da kuka kashe shi ne na ƙarshe a cikin waɗanda suke da irin fahimtarsa?
Tarihi ya sha ba mu amsar waɗannan tambayoyi, amma abin takaici, wasu mutane ba sa koyon darasi sai bayan sun aikata abin da ba za su iya gyarawa ba.
Kisan da aka yi wa malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, a Dutsin-Ma ta Jihar Katsina, tare da abokinsa Adamu Abubakar, a ranar 26 ga Oktoba, 2026, ya sake buɗe wani babban batu da ya kamata al’umma ta yi nazari a kai: Shin kashe wanda ya saɓa maka a fahimta zai kawo ƙarshen saɓanin ne, ko kuwa zai mayar da shi wata matsala mafi girma? Rahotanni sun ce ’yan bindiga ne suka harbe su a gaban gidan malamin, yayin da rundunar ’yan sanda ta ce ta fara bincike domin gano waɗanda suka aikata kisan. Har zuwa lokacin da rahotannin farko suka fito, ba a tabbatar da waɗanda suka aikata laifin ko ainihin manufarsu ba. Don haka, bai dace a ɗora laifin a kan wata ƙungiya ko mabiyan wata fahimta ba tare da sahihin bincike ba.
Duk da haka, wannan bala’i ya kamata ya zama gargaɗi ga duk wanda yake ganin cewa bambancin fahimta yana ba shi damar zubar da jinin wani. Idan aka tabbatar cewa an kashe mutum saboda ra’ayinsa ko koyarwarsa, to wannan ba nasara ba ce ga gaskiya; alama ce ta gazawar hujja da tattaunawa. Domin idan mutum ya kasa kayar da abokin hamayyarsa da dalili, sannan ya koma ga makami, abin tambaya shi ne: Wane ne ainihin abin da ya ci nasara?
A ganina, kisa ba amsa ba ne. Kisa ba hujja ba ne. Kisa kuma ba hanya ce ta tabbatar da gaskiya ba. Abin da kisa yake yi shi ne kawo ƙarshen rayuwar mutum, amma ba lallai ya kawo ƙarshen tambayoyin da ya taso ba. Wani lokaci ma, yana ƙara wa waɗannan tambayoyi nauyi, ya sa mutane su fara nazarin saƙon mamacin fiye da yadda suka taɓa yi a lokacin rayuwarsa.
Allah Maɗaukakin Sarki ya yi gargaci mai tsanani a cikin Alƙur’ani game da zubar da jinin da bai halatta ba. A cikin Suratul Isra’i, aya ta 33, Allah Ya ce; kada a kashe ran da Allah Ya haramta sai bisa haƙƙi, sannan Ya yi gargaɗi cewa ko da an zalunci wani har aka kashe shi, bai kamata a wuce gona da iri wajen neman sakamako ba.
Wannan aya tana koyar da mu abubuwa masu muhimmanci guda biyu: na farko, rayuwar ɗan Adam tana da girma, ba abin wasa ba ce. Na biyu kuma, ko wanda aka zalunta bai samu izinin yin duk abin da ya ga dama ba. Idan ma wanda aka kashe yana da haƙƙin neman adalci ta hanyoyin da Shari’a ta tanada, to ta yaya wanda ya ɗauki makami ya kashe mutum saboda saɓanin fahimta zai halatta wa kansa wannan laifi?
A Suratul Ma’ida, aya ta 32, Alƙur’ani ya bayyana girman laifin kashe rai ba tare da haƙƙi ba, ta hanyar misalin wanda ya kashe mutum kamar ya kashe dukan mutane, yayin da ceton rai kuma yake da matsayi mai girma. Wannan ba kira ba ne kawai ga tausayi; kira ne ga al’umma ta fahimci cewa rayuwa tana da darajar da ba za a iya auna ta da ra’ayi, ƙabila, ƙungiya ko saɓanin aƙida ba.
Duk wanda yake tunanin zai kashe mutum ya huta, ya kamata ya tuna cewa mutuwa ba ta jiran izinin mutum. Wanda yake da makami a yau, shi ma yana tafiya ne zuwa ga ranar da zai bar duniya. Wanda yake ganin kansa mai iko a yanzu, gobe zai iya zama wanda ake ɗauke da gawarsa. Babu wanda yake da tabbacin cewa mutuwa za ta zo masa a lokacin da ya shirya, ko a wurin da yake tsammani.
Saboda haka, abin mamaki ne mutum ya manta da nasa ƙarshen, ya dauki rayuwar wani kamar ita ce ke tsakaninsa da nasara. Kai ma za ka mutu. Ni ma zan mutu. Wanda ka ƙi, wanda ka so, wanda ka kira ɗan bidi’a ko kafiri saboda saɓanin fahimta, dukkanmu muna tafiya ne zuwa ga wannan ƙarshe. Bambancin shi ne, babu wanda ya san lokacin da zai isa, ko makomar sa a can.
Shin kashe Sayed Ali Khamenei ya kawo ƙarshen Iran?
Duniya ta ga wani babban misali a kisan Sayed Ali Khamenei, jagoran Juyin Juya Halin Addinin Musulunci na ƙasar Iran, a hare-haren sama da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, 2026. Rahotanni sun tabbatar da mutuwarsa, kuma daga baya aka zaɓi ɗansa, Mojtaba Khamenei, a matsayin wanda zai gaje shi a jagorancin ƙasar.
Mai yiwuwa masu tsara irin wannan hari su yi tunanin cewa kawar da babban jagora zai raunana tsarin da yake jagoranta, ko kuma ya haifar da ruɗani da zai sa abokan hamayyarsa su cimma manufarsu. Amma abin da ya biyo baya ya nuna cewa mutuwar jagora ba ta nufin mutuwar tsarin siyasa ko ra’ayin da yake wakilta kai tsaye ba. Iran ta ci gaba da tsarin jagorancinta, yayin da sabon jagoran ya fito da saƙon cewa ƙasar za ta nemi ɗaukar fansar mutuwar mahaifinsa da sauran waɗanda suka mutu a hare-haren. Wannan ya nuna cewa kisan ya zama wani sabon sashe maimakon kawo ƙarahen ƙasar.
To, idan manyan ƙasashe masu makamai, bayanan sirri da ƙarfin soja ba za su iya tabbatar da cewa kashe jagora shi ne cin burin su ba, me zai sa wani zan bindiga ya yi tunanin cewa kashe malamin addini saboda saɓanin fahimta zai sa jama’a su daina tunani ko tattaunawa?
Mu ɗauki misalin Imam Ali ɗan Abi Talib (AS), wanda aka kashe a shekara ta 661 Miladiyya bayan wani harin da la’ananne AbdurRahman ɗan Muljam ya kai masa. Mutuwarsa ba ta sa sunansa ya ɓace daga tarihin Musulunci ba; a maimakon haka, ta zama wani muhimmin sashe na tarihin da ake ci gaba da nazari a kansa.
Haka kuma, tarihin Annabawa yana koyar da cewa masu saƙo sun fuskanci barazana, tsangwama da yunƙurin kashe su. Alƙur’ani ya ambaci yadda wasu daga cikin Bani Isra’ila suka ƙi Annabawa, har suka kai ga kashe wasu daga cikinsu ba tare da haƙƙi ba. Wannan ya nuna cewa zubar da jinin mai saƙo ba sabon abu ba ne a tarihin ɗan Adam. Amma tambayar da ta rage ita ce: Shin waɗanda suka yi hakan sun tabbatar da gaskiyarsu ne, ko kuwa sun ƙara nuna yadda ƙiyayya za ta iya makantar da mutum har ya ƙi jin wata hujja?
Saboda haka, ya kamata mu bambanta tsakanin girmama mutum da amincewa da dukkan ra’ayoyinsa. Ba lallai ne ka yarda da Sheikh Yahaya Masussuka a duk abin da yake faɗa ba kafin ka ce bai kamata a kashe shi ba. Ba lallai ne ka yarda da Khamenei ko tsarin siyasar Iran ba kafin ka fahimci cewa mutuwar mutum ba ta zama abin da za a yi murna da shi saboda kawai yana da ra’ayin da ka ƙi. Za ka iya ƙalubalantar ra’ayi, ka rubuta martani, ka yi muhawara, ka kai ƙara ga hukuma idan an aikata laifi. Amma babu wani saɓanin fahimta da zai ba ka ikon zama alƙali da mai zartar da hukunci a lokaci guda.
Idan ka kashe abokin hamayyarka, wa ya tabbatar maka cewa ka ci nasara?
Wannan ita ce tambayar da nake son duk wanda yake tunanin kashe wani zai magance matsalarsa ya yi wa kansa. Bayan ka kashe shi fa? Shin za ka iya dawo da rayuwarsa? Za ka iya goge zubar da jininsa daga tarihin iyalinsa? Za ka iya hana ’ya’yansa, matansa, iyayensa ko abokansa jin raɗaɗin rashi? Za ka iya tabbatar wa duniya cewa ra’ayinka ne gaskiya ta hanyar kashe wanda ya saɓa maka?
A’a. Abin da za ka iya yi kawai shi ne ka jawo wata asara da ba za a iya gyarawa ba, sannan ka ɗora wa kanka nauyin laifi da sakamakonsa. Idan ka yi tunanin cewa mutuwa ita ce hanyar da za ka tabbatar da cewa kana da gaskiya, ka tuna cewa mai gaskiya ba ya buƙatar ya kashe abokin muhawararsa domin hujjarsa ta tsaya.
Ya ku masu ɗaukar makami saboda saɓanin fahimta, ku tuna: ku ma mutane ne, ba mala’iku ba. Ku ma kuna da iyalai, abokai da waɗanda suke ƙaunarku. Ku ma za ku mutu. Mutumin da kuka kashe ba shi kaɗai ne mai ƙarshen rayuwa ba; ku ma kuna da ranar da za ku bar duniya. Bambancin fahimta ba ya canja wannan gaskiya.
Kafin ku ɗaga makami, ku tuna da kabari. Kafin ku harba harsashi, ku tuna da ranar da za a hura ƙaho a kan kabarinku. Kafin ku yanke shawarar cewa wani bai cancanci rayuwa ba saboda abin da yake tunani, ku tambayi kanku ko kun mallaki rayuwar da kuke ƙoƙarin karewa.
Domin a ƙarshe, babu wanda zai rayu har abada. Wanda kuka kashe zai mutu, amma ku ma za ku mutu. Bambancin shi ne, ku na iya ƙara wa kanku laifin zubar da jinin da ba ku da haƙƙin zubarwa. Kuma abin da kuka ɗauka a matsayin nasara a yau, gobe zai iya zama abin kunya da tarihin zai riƙa tunawa da shi.
Kisa ba amsa ba ne. Harsashi ba hujja ba ne. Zubar da jini ba nasara ba ce.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.
