
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala ziyararsa a Ƙasa Mai Tsarki (Saudiyya), inda ya ce ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da nasarori a rayuwa ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani saƙo da aka wallafa ta sahihin shafinsa na X, @officialABAT inda ya bayyana ziyarar a matsayin nuna juriya kan lamuran da suka shafi imani, abota da girmama juna a tsakanin Nijeriya da Saudiyya.
A ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026 ne Shugaban Nijeriyar ya tafi Saudiyya domin gudanar da Umrah a Masallacin Harami a Makkah. A yayin haka, Shugaba Tinubu ya samu karramawar shiga daƙin Ka’abah bayan hukumomin ƙasar sun amince a buɗe masa, inda ya gudanar da wasu addu’o’i tare da yin ibadar Umarar.
Ya kuma yi godiya ga Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, @KingSalman da Yarima mai jiran gado kuma Firaminista, Mohammed bin Salman bisa ba shi damar tare da ‘yan tawagarsa da kuma walwalarsu a ƙasar.
Kazalika, ya ce yi wa Nijeriya da al’ummarta addu’o’in samun nasarori. “Na yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da nasarori ga ƙasarmu da dukkan ‘yan Nijeriya, inji shi.
