Sahabi Ya’u ya lashe zaɓen fidda gwani na APC a Zamfara ta Arewa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura ya sake lashe zaɓen fidda gwanin kujerar Sanata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na yankin Zamfara ta Arewa wanda aka gudanar a ranar Litinin.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na APC na mazaɓar Sanata ta Zamfara ta Arewa, Dr. Auwal Abdullahi Aliyu, ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin lumana, sahihi, kuma bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma dokar zaɓe.

A cewar Dr. Auwal, Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura ya samu ƙuri’a 49,176 inda ya doke abokan takararsa, Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura (OD) wanda ya samu kuri’u 9,628, da kuma Hon. Sani Abdullahi Shinkafi (Wamban Shinkafi) wanda ya zo na uku da ƙuri’a 6,206.

Dr. Auwal ya bayyana cewa dukkan masu ruwa da tsaki sun amince da zaɓen kuma ya ayyana Sanata Sahabi Ya’u a matsayin wanda ya lashe zaɓen bisa cancanta.

“Bayan cika dukkan ƙa’idojin doka da ƙa’idojin zaɓen fidda gwani na APC, ni, Dr. Auwal Abdullahi Aliyu, shugaban zaɓen fidda gwanin Sanata na APC na shiyyar Zamfara ta Arewa, ina ayyana Sahabi Ya’u Ƙaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin,” in ji shi.

Da yake bayyana yadda aka samu ƙuri’un a ƙananan hukumomi huɗu da suka haɗa yankin Sanata, Dr. Auwal ya ce zaɓen ya gudana cikin nasara.

Idan za a iya tunawa cewa wannan sabon zaɓen ya zama wajibi ne sakamakon ƙarar da ɗaya daga cikin masu takarar, Hon. Sani Abdullahi Shinkafi, ya shigar a gaban kotu akan jam’iyyar APC, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), da Sanata Sahabi Ya’u kan zargin kura-kurai da aka samu a zaɓen fidda gwani na farko da aka yi a Zamfara ta Arewa.

By ukarofi

Leave a Reply