Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙaramar hukumar Funtua, Alhaji Abdulmutallab Jibrin Sulaiman Goya, ya yi kira ga iyaye da su ƙara himma wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu a kan ilimin addinin Musulunci, musamman koyar da su karatun Alƙur’ani mai girma da haddace shi.
Goya ya yi wannan kiran ne yayin bikin rufe gasar karatun Alƙur’ani mai girma ta shiyyar Funtua, wadda aka gudanar a Makarantar Government Girls Day Secondary School da ke Funtua.
Goya wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin addinai da tsaro, Alhaji Mustapha Shata, ya bayyana cewa irin waɗannan gasa na taimakawa wajen zaburar da yara da matasa, maza da mata, su ƙara ƙaimi wajen koyon karatun Alƙur’ani da haddace shi cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya ƙara da cewa yawaita karatun Alƙur’ani na daga cikin hanyoyin da ke ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma, baya ga ladan da masu karanta littafin Allah da bin koyarwarsa suke samu a duniya da lahira.
Alhaji Abdulmutallab Goya ya kuma yaba wa shugabanni da masu gudanar da gasar tun daga matakin ƙaramar hukuma zuwa shiyya da kuma jihar Katsina, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar Funtua za ta ci gaba da ba da goyon baya da gudummawa ga harkokin irin wannan hidima.
A yayin taron, shugaban ya bayar da tallafin kuɗi naira 200,000 domin sayen ruwan sha ga ɗaliban da suka halarci gasar.
Haka kuma, ya taya waɗanda suka yi nasara a matakai daban-daban murna, tare da yi musu fatan alheri yayin da za su wakilci shiyyar Funtua a gasar matakin jiha.
A nasu jawabai, shugabannin da suka shirya kuma suka gudanar da gasar sun yi kira ga jami’an gwamnati da masu hannu da shuni da su riƙa saka jari wajen tallafa wa harkokin Alƙur’ani, domin samun lada da ribar da za ta amfani al’umma a duniya da lahira.
Sun kuma miƙa godiya ga dukkan waɗanda suka bayar da gudummawa wajen ganin an gudanar da taron cikin nasara.
Sarkin Maskan Katsina, Hakimin Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, wanda limamin babban masallacin Juma’a na Funtua, Imam Abdulrahman Jibrin, ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin masu shirya gasar wajen ganin yara sun iya karatun Alƙur’ani yadda ya kamata, sun san ƙa’idojinsa tare da haddace shi.
Ya kuma tabbatar da goyon bayan masarautar ga dukkan shirye-shiryen da suka shafi bunƙasa ilimin addini da na zamani.
Daga cikin abubuwan da suka gudana a wajen bikin akwai raba kyaututtuka ga ɗaliban da suka zo na ɗaya, na biyu da na uku a rukuni daban-daban, domin ƙarfafa musu gwiwa da zaburar da sauran mahalarta gasar.
