
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026 zakaran ɗan ƙwallon ƙafar nan na duniya, Cristiano Ronaldo ya sanar da yin murabus daga wakiltar ƙasarsa Portugal a matsayin ɗan wasa, matakin da ya kawo ƙarshen zamaninsa na tsawon shekara 23.
Ronaldo mai shekara 41 ya tabbatar da matakin ne a kafafen soshiyal mediya, inda ya ce a yanzu ya bar tawagar domin ‘yan wasa masu tasowa. Ya bayyana cewa, matakin bai kasance mai sauƙi a gare shi ba, amma zai bayar da babbar rigarsa mai ɗauke da lamba bakwai bayan kammala hutun wasannin ƙasa-da-ƙasa na watan Nuwamba.
Wannan mataki ya biyo bayan halin tsaka-mai-wuya da aka samu a tawagar a lokacin da rikici ya ɓarke tsakanin Ronaldo da kociya Jorge Jesus yayin hutun wasannin ƙasa-da-ƙasa da ya gabata. Dan wasan ya bar ciki tawagar ne bayan an sanya shi a banci a wasan Nations League, lamarin da ya sa aka dakatar da Ronaldo na wucin-gadi da cin sa tara da hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta yi a matsayin hukunci a gare shi.
A yanzu ɗan wasan zai cigaba da taka wa ƙungiyarsa ta Al Nassr leda zuwa wani lokaci, musamman duba da yadda yake harin kai matakin zura ƙwallayensa zuwa guda 1000, inda ya halin da ake ciki yana da 985.
Ronaldo ya yi adabo da ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa ne a matsayin wanda ya fi kowane ɗan wasa ƙoƙari a ɓangaren, inda ya ajiye tarihin mafi yawan wakilci a wasanni na guda 234 da kuma mafi yawan cin ƙwallo (146). Ya taimaka wa Portugal lashe kofin Euro a shekarar 2016 tare da cin kotunan Nations League a 2019 da 2025.

