MURIC ta nemi a kori Shugabar Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya kan rikicin saka hijabi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Nijeriya (MURIC) ta buƙaci a kori Darakta-Janar ta Makarantar Horar da Lauyoyi ta Nijeriya, bisa zargin nuna wariya ga ɗalibai mata masu sanya hijabi da kuma musanta cewa an hana su shiga jarrabawar ƙarshe da suke yi a halin yanzu.

Kungiyar ta kuma zargi shugabar makarantar da ɓoye ƙiyayya ga Musulmi, tana mai cewa musanta faruwar lamarin da ta yi ya ƙara tabbatar da buƙatar gudanar da bincike kan zargin.

Babban Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaƙ Akintola, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. A cikin sanarwar, Akintola ya ce Makarantar Horar da Lauyoyi ta Nijeriya ta musanta zargin nuna wariya ga ɗalibai mata masu sanya hijabi yayin jarrabawar ƙarshe da ake gudanarwa a makarantar.

Ya bayyana musantawar a matsayin abin takaici da ban mamaki, yana mai cewa ƙungiyar na da kwafin wasu rubutattun umarni da aka bayar a wasu rassa na makarantar, waɗanda ya ce sun samo asali ne daga umarnin baki da ake zargin Darakta-Janar ɗin ta bayar. A cewarsa, waɗannan takardu sun isa su tabbatar da cewa an bayar da umarnin cire hijabi, duk da cewa makarantar ta musanta hakan.

Ya kuma yi tambayar inda rassan makarantar suka samo ikon bayar da irin waɗannan umarni, tare da cewa ko Darakta-Janar ɗin ta nemi bayani daga gare su kan dalilin bayar da umarnin da ba su da izinin bayarwa. Akintola ya ce, musanta faruwar lamarin da makarantar ta yi bai kawar da zargin da ake yi ba, musamman ganin cewa ƙa’idar ɗabi’a da makarantar ta tanada wa ɗalibai, a sashe na B, ƙa’ida ta biyar, ta amince da hijabi a matsayin tufafin da ɗalibai mata Musulmi za su iya sakawa.

Ya ce, duk da wannan tanadi, ana zargin Darakta-Janar ɗin ta bayar da umarnin baki da ya saɓa wa ƙa’idar makarantar, lamarin da ƙungiyar ke ganin yana da alaƙa da ra’ayin da take da shi kan masu sanya hijabi.

ƙungiyar ta ce, tana zargin shugabar makarantar ba ta son ganin mata Musulmi sanye da hijabi, kuma tana kallon hakan a matsayin abin da ya kamata a kawar da shi. MURIC ta kuma bayyana cewa, abin da ya faru a cibiyoyin jarrabawar ya jefa ɗalibai Musulmi cikin matsanancin tashin hankali, wanda take ganin ka iya shafar yadda suka gudanar da jarrabawarsu, yayin da ɗalibai Kirista suka samu damar yin jarrabawar cikin kwanciyar hankali ba tare da wata tangarɗa ba.

A cewar ƙungiyar, kafin fara wannan taƙaddama a ranar Asabar, ɗaliban suna kallon junansu ne a matsayin abokan karatu, ba tare da la’akari da bambancin addininsu ba. Sai dai ta ce lamarin ya haifar da yanayin da zai iya kawo rabuwar kai tsakanin ɗalibai bisa addini.

Ta kuma nuna damuwa kan yiwuwar abin da ya faru ya shafi adalci wajen tantance sakamakon jarrabawar, tana mai cewa ba za a iya tabbatar da cewa an tantance ɗaliban da abin ya shafa cikin gaskiya da adalci ba bayan irin matsin lambar da suka fuskanta.

MURIC ta ce abinda ya faru ya nuna, a ganinta, cewa Darakta-Janar ɗin na da tsattsauran ra’ayi kan ɗalibai mata Musulmi masu sanya hijabi. Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci Majalisar Ilimin Shari’a ta kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan takaddamar hijabin. Ta kuma buƙaci Darakta-Janar ɗin da ta janye daga gudanar da ayyukanta a lokacin binciken, domin bai wa kwamitin damar gudanar da bincike cikin ’yanci, gaskiya da adalci.

A ƙarshe, ƙungiyar ta ce ya kamata a kori shugabar makarantar idan ba ta yi murabus da kanta ba bisa zargin jawo wa makarantar abin kunya, musanta zargin hana ɗalibai sanya hijabi da kuma kasancewa da ra’ayin ƙiyayya ga Musulmi.

By ukarofi

Leave a Reply