*Shugabancin David Mark da ya zaɓe shi haramtacce ne, inji kotu
•ƙoƙarin murƙushe ’yan adawar Nijeriya ne – ADC
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shari’ar siyasar Nijeriya ta sake shiga wani sabon babi mai cike da ruɗani bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da rusa dukkan matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027 da ke tafe.
Sai dai maimakon amincewa da hukuncin, ADC ta yi fatali da shi, tana mai zargin jam’iyyar APC mai mulki da amfani da dabaru, domin raunana ’yan adawa da kuma hana ’yan Nijeriya damar zaɓen shugabannin da suke so. Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa, za ta ƙalubalanci hukuncin a Kotun ɗaukaka ƙara, tana mai cewa, matakin ya haifar da barazana ga dimukraɗiyyar Nijeriya.
Mai shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan amincewa da ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban ADC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, ya shigar.
Gombe ya garzaya kotu ne domin ƙalubalantar yadda kwamitin riƙo na jam’iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark ya karɓi ragamar shugabancinta. Ya bayyana cewa, bayan murabus ɗin tsohon Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci ya gaje shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
A cikin ƙarar, mai ƙara ya buƙaci kotu ta soke dukkan matakan da shugabancin David Mark ya ɗauka, tare da hana Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola ci gaba da gabatar da kansu a matsayin Shugaban ADC na ƙasa da Sakataren Jam’iyyar na ƙasa, bisa zargin cewa naɗinsu ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokar zaɓe.
Kotun ta amince da buƙatun mai ƙara, inda ta bayyana kwamitin riƙo na ADC ƙarƙashin David Mark a matsayin wanda ya kafa ba bisa ƙa’ida ba, tare da soke dukkan matakan da ya ɗauka a madadin jam’iyyar.
Hukuncin ya shafi zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, kasancewar kwamitin Mark ne ya shirya zaɓen fidda gwani da ya samar da shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Tun da farko, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta wallafa sunan Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, yayin da shi kuma ya zaɓi tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.
Sai dai hukuncin kotun ya kawo sabon ƙalubale ga shirin jam’iyyar na shiga zaɓen 2027, musamman ganin cewa zaɓen shugaban ƙasa an tsara gudanar da shi ne a ranar 16 ga Janairu, 2027.
Martanin ADC da zargin APC:
A martaninta kan hukuncin, ADC ta bayyana cewa ba za ta amince da abin da ta kira hukuncin da ba shi da ingantacciyar hujjar shari’a ba, tana mai zargin APC da ƙoƙarin amfani da kotuna wajen raunana jam’iyyun adawa.
A cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Ƙasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Alhamis, jam’iyyar ta ce lokacin da aka yanke hukuncin, kwana guda kacal bayan babban taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ta gudanar a Jihar Sakkwato, ya nuna irin fargabar da take zargin APC ta shiga sakamakon ƙaruwar goyon bayan da take samu. Jam’iyyar ta bayyana cewa taron yaƙin neman zaɓenta na ranar 4 ga Nuwamba a Sakkwato ya samu halartar ɗimbin jama’a, lamarin da a cewarta ya tayar da hankalin jam’iyyar APC mai mulki.
Sanarwar ta ce, “Muna da dalilan da suka sa muka yi imanin cewa tun da daɗewa aka riga aka rubuta hukuncin wannan shari’a. Taron Sakkwato ne kawai ya zama dalilin gaggauta bayyana shi. Jiya, dubban ɗaruruwan ’yan Nijeriya sun fito domin nuna goyon bayansu ga ADC da alƙawarin da muka ɗauka na samar musu da rayuwa mai sauƙi. Amma yau, ana gaya musu cewa za a iya soke jam’iyyar da suke goyon baya da kuma ’yan takarar da suka zaɓa a dukkan matakan zaɓe, ta hanyar hukuncin kotu.”
ADC ta nuna damuwarta kan irin tasirin da hukuncin zai iya yi ga tsarin dimokuraɗiyya, tana mai cewa ba wai Atiku Abubakar da David Mark kaɗai abin ya shafa ba ne, har da dubban ’yan takarar da ke shirin neman kujeru a ƙƙnanan hukumomi, jihohi da matakin tarayya.
Ta ce, “Wannan batu bai shafi Atiku Abubakar ko David Mark kaɗai ba ne. Ya shafi haƙƙin dimokuraɗiyya na ’yan Nijeriya na zaɓen shugabannin da suke so cikin ’yanci. Haka kuma, ya shafi haƙƙin dubban ’yan takara na shiga zaɓe cikin tsarin dimokuraɗiyya.”
Jam’iyyar ta kuma dogara da wani hukuncin da Mai shari’a Musa Liman na Babbar Kotun Tarayya ya yanke a ranar 2 ga Yuli, 2026, a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1637/2025, wanda ta ce ya tabbatar da halaccin Kwamitin Gudanarwa na ƙasa ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da umartar INEC da ta amince da shugabancin.
A cewar ADC, ƙa’idar shari’a ba ta bai wa kotu mai matsayi ɗaya damar sake duba hukuncin wata kotu mai matsayi iri ɗaya ba, ko sauya shi, ko soke shi. Saboda haka, jam’iyyar ta ce tana jiran samun sahihin kwafin hukuncin kotun na yanzu domin tantance cikakken abin da ya ƙunsa da kuma umarnin da aka bayar, kafin ta ci gaba da ɗaukar matakan shari’a.
ADC ta kuma zargi APC da ƙoƙarin yin amfani da tsarin shari’a wajen danne ’yan adawa a duk lokacin da take ganin suna samun karɓuwa a wajen jama’a.
Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin Nijeriya sun fi burin kowane shugaban ƙasa ko jam’iyyar siyasa muhimmanci, tana mai cewa babu wanda ya kamata ya yi tsananin ƙoƙarin riƙe mulki har ya kai ga jefa makomar ƙasar cikin haɗari. Ta ce Nijeriya mallakin ’yan Nijeriya ce, ba ta wata jam’iyya ba, kuma shugabancin ƙasa ba gadon iyali ba ne.
A cikin sanarwar, ADC ta tambayi Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa idan yana ganin ya gudanar da mulki yadda ya kamata, me ya sa zai ji tsoron fuskantar hamayya a zaɓe? Haka kuma, ta ce idan APC na da yakinin cewa manufofinta da ’yan takararta sun samu karɓuwa a wajen jama’a, ya kamata ta amince da shiga zaɓe cikin ’yanci da adalci. Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ɓangaren shari’a da kada ya bari a yi amfani da shi wajen kafa mulkin kama-karya a Nijeriya.
Duk da zafafan kalaman da ta yi, ADC ta buƙaci mambobinta a faɗin ƙasar da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka da oda, yayin da shugabanninta ke shirin bin dukkan hanyoyin shari’a domin ƙalubalantar hukuncin.
A gefe guda kuma, jam’iyyar ta sha alwashin ɗaukaka ƙara, inda Sakataren Jinƙai na ƙasa na ADC, Nkemakolam Ukandu, wanda aka shigar cikin shari’ar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya tabbatar da cewa za a ƙalubalanci hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.
Hukuncin kotun da kuma martanin ADC sun ƙara rikita siyasar jam’iyyar gabanin zaɓen 2027, inda makomar shugabancinta da takarar Atiku Abubakar ke fuskantar sabon ƙalubale. Yanzu dai hankalin ’yan siyasa da masu bibiyar harkokin dimokuraɗiyyar Nijeriya ya koma kan matakin da kotun ɗaukaka ƙara za ta ɗauka, da kuma yadda wannan rikici zai shafi shirin ADC na fafatawa a babban zaɓen mai zuwa.
