Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta shirya gudanar da gangamin faɗakarwa a shirye shiryen fara allurar rigakafin shan Inna ga yara miliyan 2.7 jarirai zuwa watannin 59 a ƙananan hukumomi 28 da ya ƙunshi gudumomi 299 a Jihar Katsina.
Daraktan kula da shirin na hukuma lafiya a matakin farko Dokta Mukhtar Mahmud ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan wayar da kai kan mahimmancin allurar polio a faɗin Jihar.
Yace taron da ya ƙunshi ‘yan jarida,masu bautawa ƙasa da masu kafafen sadarwa ana sa ran zai ƙarfafa faɗakarwa da tattaunawa yadda za’a fadakar da al’umma game da mahimmancin allurar rigakafin shan inna.
Dr Mukhtar ya bayyana cewa gwamnatin Katsina da hukumar lafiya a matakin farko da sauran abokan hulɗa suka shirya taron a ƙoƙarin ganin an kawar da cutar tare da kare ƙananan yara daga kamuwa.
Yace ƙananan hukumomin Bindawa, Kankiya,Dutsi,Safana,Sandamu da Kusada kaɗai ne basu cikin ƙananan hukumomi da za’a gudanar da allurar.
Ana sa ran tattaunawar zai yi nazari jan nasarorin da matsalolin da akafi karo da su a baya da fita da hanyoyin da za a magance su da fito da sabbin tsare tsare da za a sami nasarar gangamin.
