IGP Disu ya bayar da umarnin kama tare da gurfanar da masu lalata fastocin kamfe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (NPF) ta yi gargaɗi kan yadda ake samun ƙaruwar lalata, yayyagewa da kuma ɓata fastoci, tutoci da allunan tallata ’yan takara da jam’iyyun siyasa a sassa daban-daban na ƙasar, gabanin babban zaɓen 2027.

Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa, a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar a Abuja ranar Laraba, rundunar ta yi Allah wadai da irin waɗannan ayyukan rashin haƙuri a siyasa, tare da gargaɗin ’yan bangar siyasa da sauran masu tayar da hankali da su dakatar da su nan take.

Sanarwar ta ce: “Domin kauce wa shakku, lalata, ɓata ko cire fastocin kamfen da allunan tallata wani ɗan takara ba bisa ƙa’ida ba na iya zama laifin ɓarna da dukiya, wanda doka ta haramta. Wannan ya haɗa da Sashe na 451 na Dokar Laifuka da Sashe na 326 na Dokar Penal, waɗanda suka tanadi laifin ɓarna.

“Bambancin siyasa ko biyayya ga wata jam’iyya ba ya bai wa kowa damar lalata dukiyar wani ɗan takara ko tauye masa ’yancin gudanar da kamfen cikin walwala.”

Rundunar ta sake jaddada cewa dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ko matsayinsu ba, suna da ’yancin samun kariya daidai wa daida a ƙarƙashin doka.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon yanke hukuncin wanda ya kamata a nuna fastocin kamfen ɗinsa ko kuma a lalata su.”

Babban Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, IGP Olatunji Disu, ya ce ya umarci kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da na Babban Birnin Tarayya (FCT) da su ɗauki matakan dakile irin waɗannan ayyuka tun kafin faruwarsu, su binciki duk rahotannin da aka shigar, tare da tabbatar da kama da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi bisa tanadin doka.

Sanarwar ta ce: “Haka kuma, masu ɗaukar nauyin siyasa da mutanen da ke ɗaukar ma’aikata, ƙarfafa gwiwa ko taimakawa wajen aikata waɗannan laifuka za su fuskanci hukunci idan hujjoji suka tabbatar da hannunsu a ciki.”

Rundunar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su gudanar da kamfen cikin lumana tare da mutunta ’yancin wasu, tana mai jaddada cewa bai kamata a lalata tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya ta hanyar rashin haƙuri a siyasa, tsoratarwa ko aikata laifuka ba.

Rundunar ’yan sandan ta ce ba za ta bari ’yan bangar siyasa da masu tayar da hankali su mayar da harkokin siyasar ƙasar fagen aikata rashin bin doka ba.

“Duk wanda ya zaɓi karya doka zai fuskanci cikakken hukuncin da ya dace da abin da ya aikata,” inji rundunar.

By ukarofi

Leave a Reply