Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Alhaji Tajuddeen Musa UAC mutum ne wanda ya gaji gwagwarmaya da fafutukar neman ilimi da harkokin kasuwanci a Nijeriya, Afirka, Turai, Asiya da sauran nahiyoyin duniya, ciki har da ƙasashen Togo, Burkina Faso da wasu ƙasashe da dama a Afirka.
Haka kuma, ya zauna na tsawon lokaci a ƙasar China da Amurka, da sauran ƙasashen duniya, a ƙoƙarinsa na gudanar da harkokin kasuwanci daban-daban kamar yadda doka ta tanada, ciki har da saye da sayar da motoci da sauran harkokin kasuwanci.
Wannan kuwa ya biyo bayan irin tarbiyyar da mahaifinsa ya ba shi. A ƙarshe, mahaifinsa, Alhaji Musa UAC, ɗan kasuwa ne a Kano wanda ya kafa kamfanoni masu suna iri ɗaya, ciki har da kamfanin gine-gine na Madaki ƙira, Madaki ƙira Motors da sauran harkokin kasuwanci.
A yanzu haka, Tajuddeen Musa shi ne Manajan Darakta na kamfanin 123 Homes & Facility Managers Ltd. Ya bayyana cewa irin abubuwan da ya koya da kuma abubuwan da ya gani a gida da ƙasashen da ya ziyarta sun ba shi ƙwarewa da sanin makama.
Ya ce yana da masaniya da fahimtar cewa idan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bai wa masu aikin gine-ginen unguwanni na zamani dama ta hanyar haɗin gwiwar zuba jari tsakanin Gwamnatin Kano, masu wannan aiki da sauran masu kuɗi, ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta jihar, za a samu alheri, amfani da riba mara iyaka ga gwamnatin, masu gudanar da ayyukan da sauran al’ummar Kano da ma wajenta.
Tajuddeen Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce shawararsa ga Gwamnatin Kano da sauran gwamnatocin da ke kishin al’ummarsu, jihohinsu da ƙasashensu ita ce su buɗe wani sashe a Ma’aikatar Ayyuka ta jihar, inda gwamnati za ta sayi kayayyakin aikin gine-gine na zamani, sannan ta gayyaci masu aikin gine-gine na zamani da masu hali domin su zuba jari a wannan aiki na haɗin gwiwa.
Ya bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwa zai samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati da masu gudanar da ayyukan, a tsarin da ake kira haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (Public-Priɓate Partnership – PPP) a Turance.
Ya ce yin hakan zai ba da damar ɗaukar matasa ’yan jihar da waɗanda ke wajenta, musamman waɗanda suka yi karatun ƙwarewa a wannan fanni, domin su ba da gudummawarsu. Hakan kuma zai bunƙasa guraben ayyukan yi, tattalin arziki, tsaro da zaman lafiya a Kano da Nijeriya baki ɗaya, kamar yadda yake faruwa a ƙasashen duniya da suka ziyarta.
Haka kuma, Tajuddeen Musa ya shawarci al’ummar da ke son sayen fili ko gini, da masu ruwa da tsaki a hukumomi da masana a wannan fanni, da su riƙa haɗa kai domin kauce wa matsalolin da kan taso a irin waɗannan ayyuka, kamar rigingimun filaye, rushewar gine-gine da sauran matsaloli.
Ya ce rashin ilimi da rashin tuntuɓar ƙwararru su ne ke haddasa irin waɗannan matsaloli, musamman idan aka yi la’akari da cewa rushewar gini na iya faruwa tun daga rodin gini, wanda ya ƙunshi matakai kusan biyar. Haka kuma, yashi da mai tsakuwa da maras tsakuwa suna da matakai daban-daban, amma rashin sani kan sa a ɗauka cewa duk iri ɗaya ne, lamarin da kan haifar da babbar matsala a harkar gine-gine.
A ƙarshe, Alhaji Tajuddeen Musa, shugaban kamfanin gine-gine na 123 Homes, ya ce suna da kyakkyawar alaƙa da Ma’aikatar Filaye da Safiyo ta Kano, KANUPDA da sauran hukumomin da abin ya shafa a harkokinsu.
