Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi masu gidaje da ke bai wa ’yan ta’adda haya, da kuma mutanen da ke karɓar baƙuncin tarurrukan shirya ayyukan ta’addanci, cewa za su fuskanci hukunci a gaban kotu bisa tanadin Dokar Hana Ta’addanci ta 2022. Gwamnati ta ce, dokar ta tanadi hukunta duk wani mutum ko ƙungiya da aka samu da hannu wajen taimakawa ayyukan ta’addanci, ciki har da shirya tarurrukan ƙulla makircin ta’addanci da samar da duk wani nau’in tallafi ga ƙungiyoyin ’yan ta’adda.
Daraktan Sashen Shari’a na Ofishin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro na ƙasa, Mijinyawa Zakari, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, kan kammala zagaye na 11 na shari’ar waɗanda ake zargi da aikata ta’addanci. Zakari ya bayyana cewa, duk wanda aka samu da laifin tallafa wa ta’addanci na iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari ko fiye da haka, yayin da bai wa ’yan ta’adda gidaje haya shi ma laifi ne da doka ta tanadi gurfanar da masu aikata shi a gaban kotu.
Ya ce, “Idan aka yi nazari mai zurfi kan Dokar Hana Ta’addanci ta 2022, za a ga cewa sashe na 11 zuwa na 33 sun tanadi laifuka iri-iri, ciki har da ayyukan da ake aikatawa a matsayin share fagen ta’addanci.”
Ya ƙara da cewa, dabarar gwamnati ita ce tabbatar da cewa an cafke duk masu hannu a harkokin ta’addanci, ba tare da la’akari da irin gudunmawar da kowannensu ke bayarwa ba. Ya ce bincike ne zai tabbatar da irin rawar da waɗanda ake zargi suka taka. A cewarsa, ko da mutum bai aikata wani mummunan abu na ta’addanci kai tsaye ba, shiga taron shirya ayyukan ta’addanci ko samar da duk wani tallafi ga ƙungiyoyin ’yan ta’adda na iya zama babban laifi a ƙarƙashin dokar. Daraktan ya buƙaci ’yan Nijeriya, musamman ’yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki, da su fahimci tanade-tanaden dokar domin sanin irin ayyukan da ake ɗauka a matsayin laifukan da suka shafi ta’addanci.
Haka kuma, ya gargaɗi kamfanoni da su guji karɓar kuɗaɗen da ke da alaƙa da ayyukan ta’addanci, yana mai cewa za a iya hukunta su ko da kuwa ba a yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da wani hari ko laifi ba. Ya bayyana cewa kamfanin da aka samu yana karɓar kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci na iya fuskantar tarar naira miliyan 200, tare da gurfanar da shugabanninsa a gaban kotu. Haka kuma, akwai yiwuwar a rushe kamfanin bisa tanadin dokar.
Zakari ya ce, “Wannan shi ne dalilin da ya sa ake buƙatar ƙara wayar da kan jama’a game da abubuwan da doka ta ɗauka a matsayin laifukan ta’addanci a Nijeriya. Karanta waɗannan sassa na dokar zai taimaka matuƙa wajen fahimtar lamarin.”
Ya shawarci ’yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki da su samo kwafin Dokar Hana Ta’addanci ta 2022, su karanta tanade-tanadenta domin fahimtar dabarun da gwamnati ke bi wajen yaƙi da ta’addanci.
