
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ayyana tsohon shugaban tsohon Kwamitin Gyaran Fansho, Abdulrasheed Maina a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo bisa ragin sa da hannu a karɓar wata kadarar sata.
Hakan na zuwa ne bayan shekaru da Babbar Kotun Tarayya ta same shi da laifin almundahanar kuɗaɗen da sauya akalar kuɗaɗen fansho. Saƙon EFCCn na kwanan nan ya karkata ne kan zargin karɓar wasu kadarorin sata. Jami’in hulɗa da jama’ar hukumar Dele Oyewale ya fitar da sanarwar a ranar Laraba.
A ranar 25 ga Oktoba, 2019 ne aka gurfar da Maina tare da ɗansa, Faisal bisa tuhume-tuhume guda 12 masu alaƙa da badaƙalar kuɗaɗe da ɓoye wasu haramtattun laifuka.
Daga bisani, Mai Shari’a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja da EFCC suka ce shari’ar da ƙunshi almundahanar Naira biliyan 2. A yayin haka ne alƙalin ya yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 61 da sharaɗin su riƙa tafiya a tare.
Haka kuma, kotun ta same shi da laifin ɓoye bayanansa na asusun bankunan UBA da Fidelity. A cewar shari’ar Maina ya yi amfani da sunayen wasu ‘yan gidansu ba tare da saninsu ba kuma yake gudanar da asusun. An ce an yi hada-hadar kuɗaɗe a asusun wajen tura musu miliyan N300, miliyan N500 da biliyan N1.5 yayin da kotun ta ce Maina ya gaza kare batun ko an yi amfani da su ne wajen munanan ayyuka.
A yanzu dai, kotun ta ayyana Maina, mai shekaru 61 kuma ɗan yankin Biu a Jihar Borno, a matsayin wanda ake nema, tana mai kira ga al’umma da su aike da dukkan wani rahoto da aka samu akansa a ofisoshinta na Ibadan, Uyo, Sakkwato, Maiduguri, Benin, Makurɗi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Fatakwal ko Abuja. Ko kuma ta lamba kamar haka: 08093322644 da kuma adireshin Imel: [email protected]. Ko ma ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wata hukuma cikin hukumomin tsaro.
