Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sabon tsarin albashi ga jami’an rundunonin sojin Nijeriya, inda aka ƙara musu albashi da tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da Gwamnatin Tarayya ta ce zai inganta walwala da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro.
Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba, kuma ana sa ran sama da jami’an soji 250,000 za su amfana da wannan ƙarin.
Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da amincewar cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
A ƙarƙashin sabon tsarin, an ƙara albashin sojoji daga muƙamin Private zuwa Babban Sajan da kashi 80 cikin ɗari.
Haka kuma, jami’ai daga muƙamin Warrant Officer zuwa Kanal za su samu ƙarin albashi da kashi 50 cikin ɗari, yayin da manyan hafsoshi daga Birgediya Janar zuwa Janar za su samu ƙarin kashi 30 cikin ɗari.
Ana hasashen sabon albashin zai kasance kamar haka:
ƙaramin jami’I (private): kusan N188,000 a wata.
Lans Koparal: kusan N202,000.
Koparal: kusan N208,000.
Sajan: kusan N226,000.
Babban Sajan: kusan N271,000.
A ɓangaren manyan jami’ai:
Muƙaddashin Laftanar: kusan N293,000.
Laftanar: kusan N420,000.
Kyaftin: kusan N488,000.
Manjo: kusan N571,000.
Laftanar Kanar: kusan N631,000.
Kanar: kusan N871,000.
Manyan hafsoshi kuma ana sa ran za su karɓi albashi kamar haka:
Birgediya Janar: kusan N976,000.
Manjo Janar: kusan N1.5 miliyan.
Laftanar Janar: kusan N2.02 miliyan.
Janar: kusan N2.8 miliyan a wata.
Sai dai majiyoyin soji sun bayyana cewa za a tabbatar da ainihin albashin kowane muƙami ne bayan gwamnatin tarayya ta fitar da cikakkun ƙa’idojin aiwatar da sabon tsarin albashin.
