Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta umarci a ƙara ƙarfafa sa ido kan motsin ƙasa bayan wata ƙaramar girgizar ƙasa da ta girgiza wasu sassan Babban Birnin Tarayya – Abuja.
Hukumar Binciken Yanayin ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta tabbatar da cewa an samu girgizar ne a ranar Talata, lamarin da ya sa gwamnati ta ƙara tsaurara bibiyar duk wani motsin ƙasa da ke kewaye da Abuja.
Ministan Raya Ma’adinai, Dele Alake, ya umarci NGSA da ta riƙa bayar da rahoton duk wani ci gaban da ake samu kan yanayin girgizar ƙasa a kowane sa’a.
A cikin wata sanarwa da Mataimakiyarsa kan Yaɗa Labarai, Lara Owoeye-Wise, ta fitar, ministan ya buƙaci mazauna Abuja su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
Ya ce an kuma umarci NGSA da ta ƙara sa ido kan duk wani motsin ƙasa a Babban Birnin Tarayya da kewaye, tare da gabatar da rahotanni akai-akai domin ci gaba da tantance halin da ake ciki, da kuma sanar da sauran hukumomin gwamnati idan buƙatar hakan ta taso.
Sanarwar ta bayyana cewa cibiyar lura da girgizar ƙasa ta NGSA da ke Utako ta gano girgizar da misalin ƙarfe 11:23:27 na safe a ranar Talata.
Hukumar ta ce girgizar ta samo asali ne daga zurfin kilomita ɗaya a ƙarƙashin ƙasa, sannan ta yi tafiyar kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar.
NGSA ta bayyana girgizar a matsayin mai rauni, tana mataki na I zuwa II a ma’aunin Mercalli, tare da jaddada cewa ba ta da ƙarfin da zai iya jawo rushewar gine-gine ko lalata dukiyoyi.
Hukumar ta ce, irin wannan girgizar ƙasa ta saman ƙasa ba ta barazana ga rayuka ko dukiyoyi, sai dai tana iya haifar da ɗan firgici saboda girgizar da ake ji.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan kariya da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai cewa za a ci gaba da sa ido sosai tare da sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu kan lamarin.
