Yaƙin neman zaɓe: Gwamnatin Zamfara ta hana bangar siyasa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta hana duk wani nau’in bangar siyasa a lokacin yaƙin neman zaɓen da ke tafe a Jihar.

Mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa Hon. Nura Sani Abdullahi ya yi wannan kalamai a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishin sa a Gusau yau Talata.

A cewar sa, tuni ofishin sa ya yi wani zama na musamman da shugabannin jam’iyyun siyasa 22 da ke jihar don faɗakar da juna yadda za a gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Hon. Nura Sani Abdullahi ya bayyana cewar ofishin sa ya jawo hankalin dukkanin jam’iyyun da su guji yin amfani da matasa don bangar siyasa a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Dukkanin shugabannin jam’iyyun siyasa 22 sun aminta da duk sharuɗan da aka zayyana masu wajen ganin an gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe cikin lumana ba tare da tashin hankali ba”. Hon. Haruna yace

A cewar sa, Gwamnatin Jihar Zamfara a shirye take wajen hana duk wani nau’in bangar siyasa a lokacin yaƙin neman zaɓe kuma mai girma gwamna Dauda Lawal zai aiwatar da yaƙin neman zaɓen sa ba tare da amfani da matasa ‘yan bangar siyasa ba.

Hakazalika ya bayyana cewar ofishin sa ya tantance ƙungiyoyin siyasa 100 masu goyon bayan Gwamna Dauda Lawal da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu don samun nasarar su a karo na biyu.

” Mun amshi ƙungiyoyin siyasa masu goyon bayan Gwamna Dauda Lawal da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu su 100 kuma za su bi lungu da saƙo wajen neman goyon bayan al’ummar jihar don samun nasarar da ake buƙata.”

Ya yi kira ga matasa da su guji yin amfani da su domin tada tarzoma a lokacin yaƙin neman zaɓe a Jihar.

A cewar sa, gwamnatin jihar a shirye take don inganta rayuwar matasa ba amfani da su cikin tawagar kamfen domin bangar siyasa ba.

Ya yi kira ga alummar jihar musamman magoya bayan gwamnatin Jihar da su kasance masu bin doka da oda musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe a faɗin jihar.

Haka kuma Hon. Nura Sani ya yi kira ga masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar da su taimaki alummar su, yana mai jaddada cewa gwamna Dauda Lawal, ya basu mukamai ne domin su zama wakilan shi a tsakanin al’ummar da suka fito ba domin ƙashin kansu ba.

By ukarofi

Leave a Reply