
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya warware batun garkuwar kwanan nan da ta auku a wani masallacin Juma’a da ke yankin Dakera, inda ya ce mutane 63 ne ‘yan bindiga suka sace yayin al’amarin.
Bago ya kuma yi watsi da batun cewa mutane 500 ne aka yi awon-gaba da su, yana mai bayyana adadin a matsayin iƙirarin da aka kambama da ke yawo a Soshiyal Mediya. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Neja ta Arewa, Abubakar Sani Bello ya ziyarce shi a Gidan Gwamnatin jihar domin jajenta masa kan mace-macen kwanan nan da al’amuran tsaro a Neja.
A cewar Bagoda da fari masallata 33 ne aka sace daga masallacin, yayin da a lokacin da ‘yan bindigar suke ƙoƙarin tserewa sai kuma suka kaɗa ƙeyar wasu mutane 30 daga wata kasuwa, wanda hakan ya sa adadin waɗanda aka sace ya kai 63. Ya ce, uku daga cikin waɗanda aka sace an kashe su yayin da kuma aka ceto wasu 14.
Bago ya koka kan halin ƙamarin rashin tsaro a sassan Jihar Neja musamman ta arewaci, inda ƙauyuka ciki har da Borgu suke fuskantar yawan lamuran garkuwa da mutane, yana mai fatan kwanan nan jami’an tsaro za su shawo kan al’amarin.
Tsohon gwamnan, wanda ya je gidan gwamnatin domin jajenta wa jihar kan iftila’in kwanan nan da ya shafi al’umma, ya ce zai kuma je yankin Borgu domin yi wa Masarautar jaje kan garkuwar.
