‘Ni ba shugaban riƙo ba ne’, Har yanzu Shugaba Tinubu ke mulki daga waje, inji Akpabio

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya bayyana cewa babu wani gurbi a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya tirje kan cewa har yanzu Shugaba Bola Tinubu ne yake mulkar Nijeriya duk da cewa ba ya cikin ƙasar.

Akpabio ya yi wannan furuci ne a ranar Talata a Jihar Akwa-Ibom a yayin da ya yi watsi da cigaba da nuna damuwa daga wasu kan cigaba da zaman Tinubu a Turai da tafiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima taron Majalisar Ɗinkin Duniya. Ya ce, Shugaba Tinubu na cigaba da aiki a matsayin shugaban Nijeriya duk cewa yana halin hutu, kuma yana cigaba da bayar da umarnin yadda ake gudanar da harkokin ƙasar daga waje.

Haka kuma, Shugaban majalisar ya yi watsi da iƙirarin cewa shi ne wanda yake riƙe da muƙamin shugabancin Nijeriya a matsayin riƙo, inda ya ce Tinubu ne ke cigaba da jagorantar harkokin mulkin Nijeriya daga inda yake.

Ya bayyana cewa, kasancewar shugaban yana halin hutunsa na shekara a ƙasar wajen, hakan ba ya nuna ya ƙaurace wa harkokin mulki ko ɗora shi a matsayin shugaban riƙo, yana mai cewa “babu gurbi. Mutanen da ke magana suna magana ne kawai. Ni shugaban Majalisar Dokokin Ƙasa ne kawai.”

Ya ƙara da cewa, ci-gaban fasaha ya taimaka wajen Shugaba Tinubu ya cigaba da bayar da umarni kan harkokin gwamnati yayin da yake waje, yana mai nuna inkarinsa kan yadda mutane suke ƙorafi akan al’amarin.

A ranar 30 ga Agusta ne Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da hutun shekara na tsawon mako uku ga shugaban, wanda ta ce zai gudanar a Nahiyar Turai, inda ya fara ya da zango a Landon kana ya garzaya zuwa Paris a ƙasar Faransa. Daga bisani, fadar ta sanar da cewa ya ƙara tsawaita hutun nasa da ‘yan kwanaki, inda ake sa ran ya dawo Nijeriya a ƙarshen mako.

By Babaji

Leave a Reply