Fitacciyar ‘yar jarida, Medina Dauda ta zama kakakin ABER

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An naɗa daɗaɗɗiyar ‘yar jarida, Hajiya Madina Dauda Nadabo a matsayin Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Shirin Ci-gaban Tattalin Arziƙin Albarkatun Ruwa na Afirka (ABER), wato Africa Blue Economy Roundtable.

Hakan na ƙunshe ne a wata takarda mai kwanan wata 15 ga Satumba, 2026, wadda Shugaban ABER kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Shirin Ci-gaban Harkokin Walwala (BTPDI) na BRACED, Dakta Piriye Kiyaramo ya sanya wa hannu.

A cewar wasiƙar, naɗin ya ya yaba da hidimar Madina Nadabo ne a matsayinta na wadda ta shafe sama da shekaru 40 tana da ƙwarewa a fannin aikin jarida da harkar yaɗa labarai a matakin ƙasa-da-ƙasa da kuma hidimarta a muƙamin Shugabar Sashe kuma Jami’ar Shirye-shiryen ta tashar Voice of America (VOA) reshen Nijeriya tun a 1998 a rassanta na Turanci da Hausa.

A sabon muƙamin nata, Nadabo za ta jagorancin sashen yaɗa labaran ABER a fannin dabaru da shirya saƙonninsa, mai magana da yawunsa, kula da labarai da harkokin hulɗa da jama’a da kuma sanya ido a sashen yanar gizo da kafafensa na Soshiyal Mediya.

Haka kuma, cikin nauye-nauyen da ke kanta akwai jagorantar alaƙoƙin shirye-shirye da gwamnati, harkokin difulomasiyya da wasu masu ruwa da tsaki da kuma kira da a dama da mata a fannin tattalin Blue Economy. Sai kuma sanya ido kan labarai da wallafe-wallafen cikin gida da jagorantar yaɗa labarai ga shirye-shirye da nasarorin ABER.

Wannan naɗi dai kamar yadda aka bayyana a matsayin na sa kai, ya fara aiki ne tun a ranar 15 ga Satumba, 2026.

By Babaji

Leave a Reply