Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kafin a fara amfani da takardun kuɗi irin waɗanda ake gani a yau, al’ummomin da ke zaune a yankin da daga baya ya zama Nijeriya sun yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen gudanar da kasuwanci da musayar kayayyaki. Daga ƙananan wuri na teku zuwa manila, gishiri da musayar kaya da kaya, tsarin kuɗi ya sha sauye-sauye kafin takardar kuɗi ta fara samun matsayi a ƙasar.
To, yaushe aka fara amfani da takardar kuɗi a Nijeriya? Wace hukuma ce ta fara fitar da ita? Kuma ta yaya ta zama hanyar biyan kuɗi a ƙasar?
Labarin ya fara ne tun kafin kafuwar Babban Bankin Nijeriya, CBN, da kuma kafin samun ’yancin kai.
Kafin takardar kuɗi:
A zamanin da, ba a dogara da takardar kuɗi ko tsabar kuɗi wajen yin ciniki a yankunan da suka haɗa da Nijeriya ta yau ba.
Mutane sun yi amfani da kayayyaki daban-daban a matsayin hanyar musayar kaya. Daga cikin waɗannan akwai wurin teku, wato cowries, manila, gishiri, da sauran kayayyaki. A wasu wuraren kuma, mutane suna musayar kaya da kaya kai tsaye, wato tsarin da ake kira barter.
Bayanan Babban Bankin Nijeriya sun nuna cewa wuri na teku ya kasance muhimmin nau’in kuɗi na gargajiya na tsawon lokaci. A tsarin da ake amfani da shi a Legas a ƙarni na 19, wuri 40 suna yin “string”, strings 50 su zama “head”, yayin da heads 10 suka zama “bag”. A shekarar 1865, jaka ɗaya da ke ɗauke da kusan wuri 20,000 a Legas ana musayar ta da fam ɗin Ingila ɗaya ko biyu.
Manila kuma, wadda aka yi ta da ƙarfe mai siffar zobe ko takalmin doki, ta taka muhimmiyar rawa a tsarin kasuwanci a wasu sassan yankin, musamman a zamanin cinikin bayi.
Amma zuwan tsarin mulkin mallaka na Birtaniya ya fara sauya wannan tsarin a hankali.
Shilling da Pence sun fara shigowa:
A shekarar 1880, wata doka ta mulkin mallaka ta samar da tsarin kuɗin da ya dogara da shilling da penny a matsayin kuɗin da doka ta amince da amfani da shi a yankunan Birtaniya na Yammacin Afirka.
A wannan lokacin, tsabar kuɗi ce ta fi rinjaye. Babban Bankin Ingila ne ke kula da wasu daga cikin tsabar kuɗin, yayin da Bank for British West Africa, wanda daga baya ya zama tushen First Bank of Nigeria, ke rarraba su a yankin har zuwa 1912.
Amma har yanzu ba a samu wata hukuma guda da ke tsara samar da kuɗin ga dukkan yankunan Birtaniya na Yammacin Afirka ba.
Wannan ne ya haifar da kafa wata hukuma mai muhimmanci a tarihin kuɗin Nijeriya.
Haihuwar West African Currency Board:
A shekarar 1912, Birtaniya ta kafa West African Currency Board (WACB), wato Hukumar Kula da Kuɗin Yammacin Afirka.
Hukumar ce ta samu alhakin samar da kuɗi da kula da yawan kuɗin da ke yawo a yankunan da Birtaniya ke mulki a Yammacin Afirka, ciki har da Nijeriya, Gold Coast — Ghana ta yau — Saliyo da Gambiya.
Daga shekarar 1912 zuwa 1959, WACB ita ce ke da alhakin fitar da tsabar kuɗi da takardun kuɗi da aka yi amfani da su a waɗannan yankuna.
Sai dai akwai wani muhimmin bayani da ya kamata a fahimta: kafa WACB a 1912 ba yana nufin an fara amfani da takardar kuɗi a Nijeriya a shekarar 1912 ba.
Takardun kuɗin WACB ba su fara fitowa ba sai 1916.
1916: Takardar kuɗi ta farko:
A cewar littafin masanin tattalin arzikin Nijeriya, R. Olufemi Ekundare, ba a fitar da takardun kuɗin Yammacin Afirka ba sai shekarar 1916.
A wannan shekarar ne aka fara fitar da takardun kuɗin WACB masu darajoji daban-daban, ciki har da fam biyar, fam ɗaya, shilling 10, shilling biyu da shilling ɗaya. An mayar da waɗannan takardu kuɗin da doka ta amince da su a yankunan Yammacin Afirka da Birtaniya ke mulki.
Wani muhimmin tarihi shi ne cewa rukunin farko na takardun kuɗin Yammacin Afirka an aika shi zuwa Legas ranar 14 ga Yuni, 1916. Wannan ya kasance muhimmin mataki a tarihin tsarin kuɗin yankin.
Saboda haka, idan ana tambayar “yaushe aka fara amfani da takardar kuɗi a Nijeriya?”, shekarar 1916 ita ce shekarar da ta fi dacewa idan ana magana kan takardun kuɗin WACB.
Amma ya kamata a lura cewa tsarin kuɗin WACB bai kasance “kuɗin Nijeriya” a ma’anar kuɗin ƙasa mai zaman kanta ba. Takardun kuɗin na British West Africa ne, kuma ana amfani da su a Nijeriya da sauran yankunan Birtaniya na Yammacin Afirka.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
