Ma’aikatan lantarki sun yi barazanar tsunduma yajin aiki kan cin zarafi daga sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Ƙasa (NUEE) a Jihar Bauchi, ta yi barazanar dakatar da ayyukan raba wutar lantarki a Nijeriya bisa zargin cin zarafin wasu mambobinta daga ɓangaren jami’an Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF).

Mataimakin Shugaban NUEE, Rilwanu Shehu ne ya bayyana haka yayin wata zanga-zangar lumana da ma’aikatan suka gudanar a Bauchi, ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026. Ya ce, sun ɗauki matakin ne domin nuna adawarsu ga kutse da cin zarafin mambobinsu da jami’an NAF suka yi.

Shehu ya bayyana cewa, a ranar 18 ga Satumba ne wasu sojoji suka afka wa ofishin Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Jos (JEDC) reshen Bauchi, inda suka zargi ma’aikatan lantarki da katse wutar ofishin NAF. A nan ne sojojin sun lakaɗa wa ma’aikata goma duka sannan suka tsare su, inda ya ƙara da cewa tun daga lokacin ma’aikatan suke karɓar magani a gidajensu.

Mataimakin Shugaban ya kuma yi kira ga ma’aikatan da su kwantar da hankali tare cigaba da kiyaye doka da oda, yana mai cewa NUEE tana aiki tare da ‘yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) domin shawo kan al’amarin.

Kazalika, ya yi barazanar cewa za su dakatar da ayyuka a baki ɗaya faɗin Nijeriya muddin ba a ɗauki matakin doka ba akan jami’an NAF da suka ci zarafin mambobin nasu, inda ya kuma ce sun bayar da wa’adin kwana uku ga hukumomi daga Litinin, 21 ga Satumba domin warware matsalar ko kuma a fuskanci halin duhu a faɗin Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply