Hukumar NELFUND tana faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ga matasa – Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yaba wa Hukumar Ba Da Lamunin Karatu ga ɗalibai ta Nijeriya (NELFUND), ya ce hukumar tana faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi Shugaban hukumar ta NELFUND, Mista Jim Oɓia, tare da Manajan Darakta/Babban Jami’in Gudanarwa na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, a Abuja ranar Talata.

A yayin ganawar, Tinubu ya yaba wa NELFUND bisa gagarumin cigaban da ta samu wajen faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ta hanyar nasarar aiwatar da Shirin Ba da Lamunin Karatu ga ɗalibai.

Haka kuma, Shugaban ƙasar ya jinjina wa jagorancin Manajan Darakta/Babban Jami’in Gudanarwa, Mista Akintunde Sawyerr, bisa yadda ya jagoranci wannan shiri tare da tabbatar da cewa miliyoyin ɗaliban Nijeriya sun samu damar samun ingantaccen ilimi ba tare da nauyin matsalolin kuɗi ba.

Ya zuwa yanzu dai, NELFUND ta raba sama da naira biliyan 303 a matsayin lamunin karatu ba tare da ruwa ba, lamarin da ya amfani fiye da ɗalibai miliyan 1.64 a faɗin ƙasar nan. Wannan babban cigaba ne wajen ciyar da Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) gaba, musamman a fannonin ilimi da bunƙasa matasa.

By ukarofi

Leave a Reply