Daga UMAR GARBA a Katsina
Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce a kusan shekaru 40 da ya shafe yana siyasa, bai taɓa ganin shugaban Najeriya mai kyawawan tsare-tsaren farfaɗo da ƙasar fiye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Masari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wasu mata a wani taro da aka gudanar a Kaduna.
Masari ya kuma soki masu cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi komai ba, yana mai cewa irin wannan suka ya taɓa faruwa a gwamnatocin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Tsohon gwamnan, ya buƙaci masu wa’azi mata da su yi amfani da tasirinsu wajen daƙile kalaman rarrabuwar kawuna, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
A watan Agustan 2026, Tinubu ya naɗa Masari a matsayin mataimakin darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen sa.
