Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan ayyukan Shirin Rigakafin Zazzaɓin Cizon Sauro na Lokacin Damina (SMC) a faɗin jihar, tare da kafa wani babban kwamitin bincike domin tantance yadda aka gudanar da shirin.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Nabilusi Abubakar K/Na’isa, ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan kafa kwamitin da aka ɗora wa alhakin gudanar da cikakken bincike kan yadda aka tsara shirin, yadda aka rarraba rigakafin da kuma yadda aka aiwatar da shi, domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ingancin gudanar da ayyukan.
Ma’aikatar ta bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take, kuma ta shafi dukkan ayyukan da ake gudanarwa a filin aiki, rabon magunguna da kuma wayar da kan al’umma, har sai kwamitin ya kammala bincikensa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an dakatar da Manajan Shirin SMC daga aiki nan take, yayin da aka miƙa ragamar tafiyar da shirin na wucin gadi ga babban jami’in da ya fi kowa matsayi a cikin shirin, domin tabbatar da ci gaba da daidaita ayyuka yayin gudanar da binciken.
Domin tabbatar da sahihanci da ƙwarewa a binciken, gwamnatin jihar ta naɗa Darakta Janar na Hukumar Yaƙi da Cutar ƙanjamau ta Jihar Kano (SACA), Dakta Usman Bashir, a matsayin shugaban kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kano (SPHCMB), Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim; Darakta Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Amfani na Lafiya (DMCSA), Pharm. Ghali Sule; Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Asibitoci (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda; Darakta Janar na Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad A. Abbas; Sakatariyar Zartarwa ta Asusun Tallafa wa Lafiya na Jihar Kano (KHETFUND), Dakta Fatima Usman Zahradden; Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA), Dakta Rahila A. Mukhtar; Mukaddashiyar Darakta Janar ta Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu, Khadijah Hussein Said, yayin da Darakta mai kula da Gudanarwa da Ayyukan Gaba ɗaya na Ma’aikatar Lafiya, Nazeer Tanko Kyaure, zai kasance sakataren kwamitin.
Ma’aikatar ta kuma umarci jami’in sa ido da tantance ayyuka, abokan hulɗar da ke aiwatar da shirin da sauran masu ruwa da tsaki da su kai dukkan takardun da suka shafi shirin zuwa hedikwatar ma’aikatar. Takardun sun haɗa da tsare-tsaren aiki da aka amince da su, bayanan rabon magunguna da kuma jerin sunayen waɗanda suka amfana, domin tantance sahihancinsu.
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da amfani da dukiyar al’umma yadda ya kamata a fannin lafiya.
Ta kuma tabbatar wa abokan hulɗar ci gaba da mazauna jihar cewa wannan bincike na da nufin ƙara inganta yadda ake gudanar da shirin, tare da tabbatar da cewa ayyukan kiwon lafiya suna ci gaba da amfanar al’ummar Kano yadda ya kamata.
Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su ba kwamitin cikakken haɗin kai domin samun nasarar aikin da aka ɗora masa.
