Zan fice daga APC idan Tinubu ya ci mutuncin limaman Cocin Katolika — Orji Kalu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, kuma Sanatan da ke wakiltar Mazaɓar Abia ta Arewa, Orji Kalu, ya bayyana cewa zai yi murabus daga jam’iyyar APC matuaar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taɓa kimar limaman Cocin Katolika.

Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya kare Shugaba Tinubu daga zarge-zargen cewa ya ci mutuncin Cocin Katolika bayan musayar kalamai da aka samu tsakanin Fadar Shugaban ƙasa da shugabannin cocin kan halin da ƙasa ke ciki.

Orji Kalu ya ce, babu ƙamshin gaskiya a iƙirarin cewa Shugaba Tinubu yana adawa da Cocin Katolika, yana mai jaddada cewa shugaban ƙasar ya daɗe yana da kyakkyawar alaƙa da cocin, tare da mutunta rawar da take takawa wajen bayyana ra’ayinta kan al’amuran ƙasa.

Ya bayyana cewa, Taron Limaman Cocin Katolika na Nijeriya (CBCN) ya daɗe yana zama murya da lamirin ƙasa ta hanyar faɗar gaskiya kan matsalolin da ke addabar ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da gwamnatin da ke kan mulki ba.

A cewarsa, “Shugaba Tinubu bai ci mutuncin Cocin Katolika ba. Wannan ba shi ne karo na farko da shugabannin cocin za su gana da shugaban ƙasa ba. A ƙasashe da dama kamar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Angola da Afirka ta Kudu, Cocin Katolika da sauran coci-coci suna taka rawa wajen faɗar gaskiya game da halin ƙasa.”

Kalu ya ƙara da cewa, CBCN ta saba fitar da matsayarta kan yanayin ƙasa tun daga lokacin mulkin soja, saboda haka bai kamata a ɗauki irin waɗannan bayanai a matsayin adawa da kowace gwamnati ba. Ya ce, bai ga wani abin da Kadinal John Onaiyekan ya faɗa da ya saɓa ba, yana mai cewa limaman Katolika sun daɗe suna bayyana ra’ayinsu kan matsalolin ƙasa a duk lokacin da suka ga dacewa.

Sanatan ya kuma ce Shugaba Tinubu ba barazana ba ne ga mabiya Katolika, domin a cewarsa yana da kyakkyawar alaƙa da shugabannin cocin. Ya ƙara da cewa, akwai abubuwan da ‘yan siyasa ba za su iya faɗa wa shugaban ƙasa ba, amma limamin Katolika zai iya faɗa masa ba tare da tsoro ba.

Har ila yau, Kalu ya yi watsi da ra’ayin cewa Shugaba Tinubu na da niyyar kawo cikas ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Ya ce shugaban ya sha alwashin gudanar da zaɓe cikin ‘yanci da adalci ba tare da tsoratar da kowa ba.

Ya ce, “Ranar da Shugaba Tinubu ya nuna rashin mutunci ga limaman Cocin Katolika, zan yi murabus daga APC.”

Wannan furuci na zuwa ne bayan cece-kucen da suka biyo bayan kalaman Babban Limamin Cocin Katolika mai ritaya na Abuja, Kadinal John Onaiyekan, wanda ya bayyana damuwarsa kan taɓarɓarewar tattalin arziki da matsalar tsaro yayin wata ganawa da Shugaba Tinubu

Martanin da wasu masu taimaka wa shugaban ƙasa a fannin yaɗa labarai suka mayar ya jawo suka daga wasu ‘yan Nijeriya, inda aka zarge su da nuna rashin mutunci ga Kadinal ɗin da kuma Cocin Katolika.

Da yake magana kan babban zaɓen shekarar 2027, Orji Kalu ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai sake samun nasarar komawa kan mulki karo na biyu. A cewarsa, gwamnatin APC ta aiwatar da ayyuka masu yawa, amma ba ta yi nasarar isar da su yadda ya kamata ga ‘yan Nijeriya ba, musamman a fannonin gine-ginen more rayuwa, tsaro da sauye-sauyen tattalin arziki. Ya ce, gwamnatin Tinubu ta cika kusan kashi 65 cikin 100 na manufofinta tun bayan hawanta mulki, yana mai hasashen cewa zuwa watan Satumba ko Oktoba, wannan ƙima za ta kai kusan kashi 70 cikin 100.

By ukarofi