Sarkin Musulmi ya buƙaci a binciki zargin kashe Kanal Abdulkarim

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci gwamnatin tarayya da rundunar sojojin Nijeriya su gudanar da cikakken bincike kan zargin kisan jami’in soji, Kanal Abdur-Razaƙ AbdulKarim Ode, tare da tabbatar da cewa an gano waɗanda ke da hannu a lamarin kuma an hukunta su bisa doka.

A cikin wata sanarwa da Yarima Bashir Adefaka ya fitar a madadin tawagar yaɗa labaran Sarkin Musulmi, Sarkin ya bayyana damuwarsa kan yadda aka ce an harbe Kanal Ode a gidansa da ke Abuja, yana mai cewa wajibi ne a gano haƙiƙanin abin da ya faru.

Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ya ce dole ne gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da adalci ta hanyar gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

Ya ce Musulunci na koyar da zaman lafiya, haƙuri, soyayya da zaman tare cikin mutunta juna, yana mai jaddada cewa waɗannan su ne ginshiƙan zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Sarkin ya bayyana marigayi Kanal AbdulKarim Ode a matsayin ƙwararren jami’in leƙen asirin soja wanda ya samu girmamawa daga al’ummar Musulmi da sauran jama’a, musamman a yankinsa.

Ya kuma buƙaci a binciki rahotannin da ke nuna cewa an yi yunƙurin kai hari ga wasu daga cikin iyalan marigayin, yana mai cewa bai kamata a bar mutuwar kowane ɗan Nijeriya ba tare da gano gaskiya da hukunta masu laifi ba.

Baya ga lamarin Kanal Ode, Sarkin Musulmi ya yi Allah-wadai da kalaman ƙiyayya da hare-haren da ake yi wa ƙananan ƙabilu da mabiya addinai a wasu sassan ƙasar nan, yana mai gargadin cewa irin waɗannan ɗabi’u na barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi soyayya, haƙuri, juriya da mutunta juna, yana mai cewa bambance-bambancen da ke tsakanin al’umma ya kamata su kasance wata hanya ta ƙarfafa haɗin kai, ba ta rarrabuwar kawuna ba.

A ƙarshe, Sarkin Musulmi ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayi Kanal Abdur-Razaƙ AbdulKarim Ode, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi.

By ukarofi

Leave a Reply