Sanata Ogoshi ya bayyana dalilinsa na barin jam’iyyar ADC

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya 

Sanata Ogoshi Onawo mai wakiltar mazaɓar sanatan Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewa ya bar Jam’iyyar African Democratic Congress ADC ne saboda zaɓen fidda gwamnan jam’iyyar bai kasance cikin gaskiya da adalci ba.

Onawo wanda a kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Allied People’s Movement APM bayan ya sha kaye a zaɓen fidda gwamin ADC ɗin a hannun James Angbazo a kujerar gwamnan jihar na 2027 mai zuwa yace da an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci da zai karɓi sakamakon.

Da yake tattaunawa da manema labarai a gidansa dake Lafiya ranar Laraba sanatan ya zargi cewa an cika zaɓen da rashin daidaito kuma ba a baiwa dukkan ‘yan takara damar fafatawa daidai ba.

“In ka shiga gasa ka sha kashi to ka san hukuncin Allah ne. Amma abin da ya faru ba hukuncin Allah ba ne.  

Hannun mutum ne da yake ƙoƙarin yin aikin Allah. Na ga wannan ba wuri ne da zan iya ci gaba da zama ba shi ya sa na bar ADC,” in ji.

Sanata Onawo ya kuma jaddada cewa zaɓen gama-gari na shekarar 2027 ba zai kasance na jam’iyyar siyasa ba sai na mutum da tarihin sa da abin da ya yiwa al’umma.

“Zaɓen 2027 ba zai zama na jam’iyya ba. Zai zama tsakanin ɗan takara da jama’a.  

Tarihin ka ne abin da ka yi abin da kake yi yanzu da abin da kake alƙawarin yi tare da taimakon Allah ne zai ba ka nasara,” in ji shi.

Sanatan ya buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da su guji siyar da ƙuri’unsu a zaɓen 2027 yana mai gargadin cewa zabar shugabanni mara kyau saboda kuɗi zai haifar da sakamako mai muni wanda zai ɗauka tsawon lokaci.

Daganan sai ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Nasarawa da su bai wa ‘yan takara da ke da ƙarfi da jajircewar kawo cigaba goyon baya maimakon ‘yan siyasar da ke son sayan ƙuri’u da jinginar da makomar jihar.

By ukarofi

Leave a Reply