
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta gurfanar da ɗaya daga cikin tsofaffin jami’anta mai suna Nwaogu Ezeakolam a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin sa da danganta kansa da ƙungiyar ta’addanci ta ‘yan fafutukar kafa ƙasar Biafara IPOB.
Rahotanni sun bayyana cewa, Daraktan kula da Shari’o’in Gwamnatin Tarayya (DPPF), Rotimi Oyedepo ya shigar da ƙarar, inda aka gurfanar da Ezeakolam a gaban Mai Shari’a Mohammed Umar bisa tuhumarsa da hannu a laifuka huɗu na zargin zama mamban IPOB da kuma wasu da suka saɓa wa dokokin haramcin ta’addanci na 2022 da 2015, waɗanda aka yi wa gyara.
Daga cikin zarge-zargen da ake tsohon jami’in na DSS akwai tuhumar sa da bayar da tallafi da tallafin kayan aiki ga IPOB, wanda ya ci karo da Sashe na 13 na Dokar dakatarwa da haramcin ta’addanci ta 2022.
Haka kuma, ana tuhumar sa da shiga ƙungiyar IPOB duk da cewa ana zargin ya san cewa an ayyana ta a matsayin ta ta’addanci, laifin da DSS ta ce ya saɓa wa Sashe na 25.
Bugu da ƙari, ana zargin sa da wallafa saƙonni a Soshiyal Mediya da nufin wayar da kan al’umma akan su shiga ƙungiyar, wanda yin hakan saɓa wa Sashe na 26 ne na kundin na 2022.
A cewar DSS, laifukan da ake tuhumar tsohon jami’in da aikatawa sun saɓa wa Sashe na 18 na kundin 2015 kuma akwai hukunci akansu.
Yayin da aka karanta masa waɗannan tuhume-tuhume, Ezeakolam ya musanta hannu a aikata dukkan laifukan.
Daga nan ne alƙalin ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba da kuma umartar a kai shi gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da za a sake zama kan shari’ar.
