Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (NSCDC) ta hukunta jami’anta 79 bisa laifuka daban-daban, tare da kama mutane 18 da ake zargi da lalata bututun mai, barnata muhimman kayayyakin gwamnati da kuma safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Babban Kwamandan NSCDC, Ahmed Audi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Abuja. Kakakin rundunar, Babawale Afolabi, ne ya wakilce shi.
Audi ya ce an kammala hukuncin jami’ai 75, yayin da wasu huɗu ke ci gaba da fuskantar matakan ladabtarwa kan zarge-zarge daban-daban.
Ya ce cikin jami’an da aka hukunta akwai Mataimakin Babban Kwamanda guda ɗaya (ACG), Mataimakan Kwamanda biyu, manyan jami’ai 35 da kuma ƙananan jami’ai 37.
A cewarsa, laifukan sun haɗa da zamba wajen ɗaukar aiki, ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba, almundahanar kuɗi, yi wa aiki zagon ƙasa, sata, sakaci, rashin gaskiya, yawan rashin zuwa aiki da sauran laifukan karya dokokin aiki.
Ya ce hukuncin da aka yanke ya haɗa da kora daga aiki, ritaya dole, da kuma mika wasu ga hukumomin shari’a domin gurfanar da su inda aka samu hujjojin aikata laifi.
Audi ya bayyana cewa jami’ai 37 an kore su daga aiki, ciki har da jami’ai biyu na rundunar Mining Marshals da ke da alaƙa da wani lamari da ya faru a Jihar Nasarawa a watan Fabrairu, wanda ya yi sanadin mutuwar kwamandansu.
Ya ce bincike ya nuna ba su da niyyar aikata laifin tun farko, amma sun karya ƙa’idojin aiki ta hanyar tunkarar masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da makamai ba tare da izini ba.
“Abin da suka aikata babban laifi ne na rashin ɗa’a, sakaci da karya dokokin aiki,” inji shi.
Ya ƙara da cewa binciken ya wanke Kwamandan Mining Marshals, John Onoja, babban mai gabatar da ƙara da sauran jami’an gudanarwa daga duk wani zargi.
Audi ya kuma gabatar da wasu jami’ai huɗu da ke fuskantar matakan ladabtarwa, ciki har da uku da aka turo daga Rundunar Sojin Nijeriya bisa zargin safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, yayin da na huɗun ke fuskantar zargin sakaci da rashin ɗa’a kan yadda ya mu’amala da wata yarinya mai aikin gida.
Ya umarci a gaggauta kammala dukkan shari’o’in ladabtarwa tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifin aikata laifi a gaban kotu.
Audi ya jaddada cewa jami’an da ake zargi har yanzu suna da cikakken haƙƙinsu na doka har sai an tabbatar da laifinsu a hukumance.
Ya kuma roƙi ‘yan Nijeriya da kada su ɗauki laifukan wasu jami’ai a matsayin halayen dukkan rundunar, yana mai cewa NSCDC za ta ci gaba da tabbatar da ƙwarewa, gaskiya da riƙon amana.
A wani ci gaba, ya ce jami’an NSCDC sun kama wasu mutane huɗu a Sabon Wuse da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) yayin da suke jigilar kayayyakin layin dogo da ake zargin sun lalata.
Ya ce za a gurfanar da su kan haɗa baki wajen aikata laifi, lalata dukiyar gwamnati, ayyukan ta’addanci da kuma mallakar kayayyakin sata.
Haka kuma, an kama wasu mutum biyu a Angwa Dudu da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada bisa zargin lalata kayayyakin wutar lantarki.
Audi ya ce rundunar ta kuma kama fararen hula shida kan zargin safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, bayan wani samame na sirri da aka gudanar a jihohin Enugu da Ebonyi.
Ya bayyana cewa an ƙwato bindigogi, alburusai, bindigun hannu, na’urorin sadarwa, kayan aikin soja da wasu kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargin.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da tsare su yayin da bincike da matakan shari’a ke gudana.
A ƙarshe, Audi ya buƙaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin ƙarfafa tsaro, gaskiya da amincewar jama’a.
