Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta kama mutane 16 da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ƙwato bindigogi 10 na nau’o’i daban-daban a cikin makonni biyu da suka gabata.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Kaduna.
Ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutum uku da ake zargi da safarar makamai, da kuma mutum shida da ake zargi da kasancewa cikin wata ƙungiyar masu safarar kuɗaɗen bogi.
A cewarsa, jami’an sun kuma ƙwato takardun dalar Amurka bogi guda 170, na’urorin solar inɓerter guda 190, mota ɗaya da aka sace, buhuna 83 na miyagun ƙwayoyi da ake zargi, wayoyin hannu 32 da aka sace, talabijin guda biyu, shanu 410 da aka sace da sauran kayayyakin da ake zargi.
Kwamishinan ya ce a ranar 21 ga Yuli jami’an ‘yan sanda sun kama Aisha Barau mai shekara 20 daga ƙauyen Ramin Kura yayin da ake zargin tana ƙoƙarin canja dalar Amurka bogi zuwa naira.
Ya ce bincike ya kai ga kama Abdullahi Muhammad mai shekara 55 da Danbala Jibrin mai shekara 57, dukkaninsu mazauna ƙauyen Ramin Kura, waɗanda ake zargi da hannu a wannan ƙungiyar.
Ya ƙara da cewa binciken ya kai ga kama wasu ƙarin mambobin ƙungiyar.
Rabiu Muhammad ya ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun kama wasu mutum uku a Jos, Jihar Filato, ranar 25 ga Yuli bayan samun sahihan bayanan sirri kan wata ƙungiyar masu safarar makamai.
Ya bayyana sunayensu da Luka Samuel mai shekara 38, John Paul mai shekara 37 da Musa Elisha mai shekara 28.
An ƙwato bindigogi biyu ƙirar gida daga hannunsu.
A cewarsa, waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna kai wa ‘yan bindiga makamai da alburusai, kuma suna taimakawa jami’an tsaro da bayanan da za su kai ga cafke sauran mambobin ƙungiyar.
Kwamishinan ya ce haɗin gwiwar jami’an ‘yan sanda na sashen Anchau da jami’an sa-kai na Yan Sa Kai sun kama Abdullahi Mohammed, wanda aka fi sani da Aala, mai shekara 34, a ranar 24 ga Yuli.
Ana zarginsa da hannu a hare-haren garkuwa da mutane da dama.
Ya ce an ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da harsasai biyar masu rai daga hannunsa.
Ana zargin ya jagoranci sace mutane a ƙauyen Kuzuntu da ke ƙaramar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna da kuma wasu yankunan makwabciyar Jihar Kano.
Rabiu Muhammad ya ce jami’an sun ƙwato wata motar Toyota Sienna da aka sace daga Masallacin Juma’a da ke Unguwan Rimi a Kaduna.
An kuma kama mutum biyu da ake zargi da satar motoci da ƙera maɓallan bogi.
Haka kuma, ya ce jami’an sun ƙwato shanu 80 da tumaki 10 da aka sace daga ƙauyen Damanko da ke ƙaramar Hukumar Zariya bayan musayar wuta da waɗanda ake zargi.
Ya ce masu shanun biyu sun samu raunukan harbi yayin harin kuma suna karɓar magani.
Kwamishinan ya ce jami’an sun ƙwato na’urorin solar inverter guda 190 da darajarsu ta kai kusan naira miliyan 69, da kuma batirin lithium guda 10 da darajarsu ta kai kusan naira miliyan 9 daga wani rumbun a Zariya.
Binciken farko ya nuna ana zargin an sace kayayyakin ne daga wata kwantena da ke jigilar su zuwa birnin.
Ya kuma ce jami’an sun kama mutum biyu da ake zargi da samar wa ‘yan bindiga miyagun ƙwayoyi a yankin Kasuwar Magani, inda aka ƙwato miyagun ƙwayoyi masu yawa.
‘Yan sanda sun nemi haɗin kan al’umma
Rabiu Muhammad ya yaba wa jami’an da suka gudanar da waɗannan ayyuka saboda ƙwarewa da jarumtaka.
Ya tabbatar wa al’ummar Kaduna cewa rundunar za ta ci gaba da murƙushe ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin jihar.
Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci, yana mai cewa rundunar na aiki tare da sojoji, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS), Hukumar NSCDC, ƙungiyoyin sa-kai da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta tsaro a Jihar Kaduna.
