BUKSWA ta ƙulla yarjejeniya da WOFAN domin bunƙasa tattalin arzikin matan ma’aikatan BUK

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

ƙungiyar Matan Ma’aikatan Jami’ar Bayero Kano (BUKSWA) ta sanar da fara haɗin gwiwa da ƙungiyar Women Farmers Advancement Network (WOFAN) domin inganta tattalin arziki da rayuwar mambobinta ta hanyar noma, sarrafa amfanin gona da sauran harkokin kasuwancin noma.

An cimma wannan matsaya ne a wani taron dabaru da aka gudanar a hedikwatar WOFAN, inda shugabannin BUKSWA suka gana da wadda ta kafa WOFAN kuma Jakadiyar ƙasa da ƙasa, Hajiya Dakta Salamatu Garba, domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa a ƙarƙashin shirin Skills Improvement to Boost Livelihood and Nurture Growth (SIBLING) da ake aiwatarwa tare da Jami’ar Bayero Kano.

Sakatariyar BUKSWA, Hajiya Halima Sadiya Mahmoud, ta ce an farfaɗo da ƙungiyar a shekarar 2024 bayan ta shafe wani lokaci ba ta aiki.

Inji ta, binciken da ƙungiyar ta gudanar ya nuna cewa da dama daga cikin mambobinta na fuskantar matsalolin rashin aikin yi, zaman gwauruwa da kuma matsin tattalin arziki, lamarin da ya sa suka fara neman haɗin gwiwar da zai samar musu da hanyoyin dogaro da kai.

A nata jawabin, Mataimakiyar Shugabar BUKSWA, Hajiya Binta Saji, ta ce ƙungiyar ta ƙunshi mata masu aiki, matan ma’aikatan da suka yi ritaya, marasa aikin yi da kuma zawarawa.

Ta ce shirin haɗin gwiwar zai samar da horo da tallafi bisa buƙatun kowane rukuni domin bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.

Da take jawabi, Hajiya Dakta Salamatu Garba ta tabbatar da cewa WOFAN a shirye take wajen gina haɗin gwiwa mai ɗorewa da zai haifar da ci gaba mai ma’ana ga mambobin ƙungiyar.

Ta buƙaci BUKSWA ta ƙarfafa tsarinta, ta tattara cikakken bayanan mambobinta tare da tantance fannonin noma da suke sha’awa kafin fara aiwatar da shirin, wanda ake sa ran zai fara kafin ƙarshen watan Agustan 2026.

By ukarofi

Leave a Reply