‘Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Sakkwato, ana fargabar an kashe mutane da dama

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ana fargabar mutuwar mutane da dama tare da sace wasu 37 a sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a ƙananan hukumomin Kebbe, Sabon Birni da Shagari na Jihar Sakkwato, yayin da wani Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda (ASP), Bala Wakili, ya rasa ransa a fafatawa da maharan.

Rahotanni sun nuna cewa marigayi ASP Bala Wakili, wanda ke aiki da Rundunar ‘Yan Sandan Kebbe, ya mutu ne ranar Litinin bayan wata arangama mai zafi tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga a yankin Kebbe.

Majiyoyi sun ce maharan sun kai farmaki ƙauyukan Girkau da Zugu da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, inda suka sace dabbobi masu yawa.

Bayan haka, haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi ‘yan sanda, sojoji da jami’an Sokoto Community Guard Corps ta yi musu kwanton bauna yayin da suke barin ƙauyen Zugu.

An ce musayar wuta ta ɗauki fiye da awa guda, amma saboda yawan maharan, sun yi galaba kan jami’an tsaro, inda suka kashe ASP Bala Wakili tare da ƙona motocin sintiri guda biyu, ɗaya ta ‘yan sanda da ɗaya ta Sokoto Community Guard Corps.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da rasuwar jami’in, yana mai cewa ya sadaukar da ransa wajen kare ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin daƙile ƙarin hare-hare.

A wani hari daban da aka kai ƙauyen Tsamaye da ke ƙaramar Hukumar Sabon Birni, ana fargabar mutane 21 sun mutu, yayin da aka yi garkuwa da mutum 37.

Mazauna yankin sun ce harin ya fara ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare ranar Litinin, kuma ya ci gaba har bayan ƙarfe 3:00 na safiyar Talata.

An ƙone gidaje biyu, an sace dabbobi, yayin da galibin mazauna ƙauyen suka tsere.

Yayin da mutane ke ƙoƙarin tsallaka kogi domin gudun harin, wani jirgin ruwa da ya yi lodin fiye da ƙima ya kife, inda mutane kusan 25, mafi yawansu mata da yara, suka faɗa cikin ruwa.

An ceto mutum bakwai da ransu, yayin da har yanzu ake neman wasu 18 da suka ɓace.

Wani mazaunin yankin ya ce bayan sun kira ‘yan uwansu ta waya, sai ‘yan bindigar suka amsa wayar tare da sanar da su cewa su ne suka yi garkuwa da mutanen.

Ya ƙara da cewa mafi yawan waɗanda aka sace mata da yara ne, har ma ya ga yadda maharan suka ajiye jarirai uku a ƙasa kafin suka tafi da iyayensu mata.

Mazauna yankin sun zargi jami’an tsaro da rashin isowa da wuri duk da an sanar da su kafin maharan su kammala harin.

Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Ayuba Hashimu, ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai ya ce har yanzu ana tantance adadin waɗanda suka mutu.

A ƙaramar Hukumar Shagari kuma, mazauna yankin sun ce kimanin ƙauyuka 20 sun zama kufai bayan wani sabon harin ‘yan bindiga.

An ce maharan sun sace dabbobi da babura, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankuna da dama tserewa saboda fargabar sake kai hari.

Gwamnatin jihar ta ce tana ci gaba da ƙarfafa jami’an tsaro, inda ta samar da motocin sulke 62 da sama da babura 300 domin yaƙi da ‘yan bindiga.

Masanin harkokin tsaro, Farfesa Murtala Rufa’i, ya danganta ƙaruwar hare-haren da damina, matsin lambar sojoji a wasu yankuna da kuma bullowar sabbin shugabannin ‘yan bindiga.

Ya kuma yi gargaɗin cewa akwai alamun haɗin gwiwa tsakanin ‘yan bindiga da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Ya ba da shawarar ƙarfafa martanin gaggawa na jami’an tsaro tare da amfani da dabarun tattara bayanan sirri, haɗin kan al’umma da inganta rayuwar jama’a domin magance tushen matsalar.

Rahotanni sun nuna cewa daga ranar 29 ga Yuni zuwa 4 ga Agusta, 2026, sama da mutum 77 sun rasa rayukansu a hare-haren ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Sabon Birni, Rabah, Bodinga, Wurno, Tambuwal, Goronyo da sauran sassan Jihar Sakkwato.

Sabbin hare-haren sun ƙara tayar da hankalin al’umma, musamman mazauna yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga duk da matakan tsaro da ake ci gaba da ɗauka.

By ukarofi

Leave a Reply