AIG Garba Ahmed ya yi wa Jami’ar KHAIRUN alƙawarin cikakken goyon bayan ‘yan sanda

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG) mai kula da Shiyya ta Daya da ke Kano, Garba Ahmed, ya tabbatar wa Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu (KHAIRUN) da ci gaba da ba ta cikakken goyon baya domin tabbatar da ingantaccen tsaro da samar da yanayi mai kyau na koyarwa, koyo da ci gaban al’umma.

AIG Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdulrashid Garba, ya jagoranci tawagar jami’ar zuwa hedikwatar Shiyya ta Daya da ke Kano domin ziyarar girmamawa.

A jawabinsa, Farfesa Abdulrashid Garba ya ce jami’ar na da kyakkyawar alaƙa da rundunar ‘yan sanda ƙarƙashin Shiyya ta Daya, wadda ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a harabar jami’ar.

Ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce gabatar da manufofi, nasarori da shirye-shiryen ci gaban jami’ar, tare da neman a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

Inji shi, haɗin gwiwar da ke tsakanin jami’ar da rundunar ‘yan sanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantaccen yanayin karatu da gudanar da ayyukan jami’ar cikin lumana.

Da yake mayar da martani, AIG Garba Ahmed ya yaba da ziyarar, yana mai cewa ta zo a kan lokaci kuma ta ba shi damar fahimtar irin ci gaban da jami’ar ke samu da kuma hangen nesan waɗanda suka kafa ta.

Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa Jami’ar KHAIRUN na da kyakkyawar makoma wajen zama ɗaya daga cikin fitattun jami’o’in Nijeriya.

Inji AIG Garba Ahmed, rundunar ‘yan sanda ta Shiyya ta Daya za ta ci gaba da bai wa jami’ar cikakken haɗin kai da goyon baya domin tabbatar da tsaro, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma samar da yanayin da zai ba da damar bunƙasar ilimi.

Ziyarar ta ƙare da musayar kyaututtukan tunawa da ɗaukar hoton haɗin gwiwa tsakanin shugabannin jami’ar da manyan jami’an rundunar ‘yan sanda.

By ukarofi

Leave a Reply