Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ayyana shugaban ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP), Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa (Wali), da mataimakinsa, Amirul Jaish Muhammad Jidda, a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo, bayan bayanan sirri da aka samo daga na’urorin fasaha da aka ƙwato a hare-haren da aka kai kan ƙungiyar a yankin Tafkin Chadi.
Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai (OPHK), Kyaftin Muhammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce an gano shugabannin ne bayan binciken ƙwararru (forensic analysis) da aka gudanar kan na’urorin da sojoji suka ƙwato, ciki har da wasu muhimman bayanan sirri da kuma kyamarar bidiyo (camcorder).
Ya ce wannan nasarar ta biyo bayan hare-haren da dakarun Operation Hadin Kai suka kai kan mayaƙan ISWAP/ISIS a yankin Tafkin Chadi da ke Arewacin Jihar Borno.
A cewarsa, mayaƙan ISWAP na amfani da kyamarar bidiyon da aka ƙwato wajen shirya bidiyoyin farfaganda da kuma ɗaukar bayanan ayyukansu.
Sanarwar ta ce binciken da aka gudanar kan na’urorin ya samar da muhimman bayanan sirri da suka taimaka wajen gano wuraren da shugabannin ISWAP ke ɓoye da kuma tantance manyan kwamandojinsu da ke aiki a yankin Mangari–Metele–Dogon Chukun da ke kusa da Tafkin Chadi.
An bayyana cewa yankunan suna cikin ƙananan Hukumomin Abadam da Kukawa na Jihar Borno.
Daga cikin waɗanda aka gano akwai Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa (Wali), wanda rundunar ta bayyana a matsayin shugaban ISWAP a yankin Afirka ta Yamma, da mataimakinsa Amirul Jaish Muhammad Jidda, wanda aka fi sani da “The One-Handed Man”, da kuma Hamad Abu Hanifa, Amirul-Fiya na ISWAP.
Goni ya ce rundunar na bai wa jama’a muhimmanci wajen neman bayanai kan Abu Musa Al-Mangawi, wanda ta bayyana a matsayin shugaban ISWAP da aka fi nema ruwa a jallo a yankin Tafkin Chadi.
Ya ce rundunar za ta bayar da tukuici mai tsoka ga duk wanda bayanansa suka kai ga kama shugaban ƙungiyar.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta kare sirrin duk wanda ya bayar da sahihan bayanai, tare da ɓoye bayanansa bisa ƙa’idojin tsaro.
Ta kuma buƙaci al’umma su ci gaba da tallafa wa yaƙi da ta’addanci ta hanyar bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin gano inda waɗanda ake nema suke.
Sai dai rundunar ta gargaɗi jama’a da kada su yi yunƙurin kama ko tunkarar waɗanda ake nema da kansu, tana mai cewa hakan na iya jefa rayuwarsu cikin haɗari.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da rundunar ke ci gaba da ƙara zafafa hare-hare kan ISWAP da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Rahotanni sun kuma nuna cewa an sanya tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda bayanansa suka kai ga kama Ibn Muhammad, kwamandan sashen Amniyya na ISWAP, yayin da aka ware Naira miliyan 10 ga duk wanda bayanansa suka kai ga kama Muhammad Jidda, wanda kuma ke jagorantar rundunar Jaish ta ƙungiyar.
